Babban Faston Cocin Latter Rain Assembly a jihar Legas, Fasto Tunde Bakare ya yabi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari akan nasarar data ke samu akan ta’addanci. A wata fira da yayi da gidan Talabijin Channels, Bakare ya bayyana cewa ba za’a kira gwamnatin Buhari wadda bata san abunda take yi ba. Ya bayyana cewa canjin Hafsin soja da yayi da kuma ziyarar da yayi ma makwabtan Najeriya abu ne Mai kyau.
Yace: “Ba zaka iya ce ma gwamnatin nan wadda bata san abun da take yi ba, sai dai kace taba neman taimako. Saboda canjin Hafsin soja, ziyarar makwabta da kuma kasashen yamma anyi haka ne saboda ya magance ta’addanci.”
Bakare kuma ya bayyana cewa Buhari ya dauki lokacin shi ne domin ya zabi mutanen da zaya iya aiki dasu.
Yace: “Ni ban ga wani abu ba cikin zaben ministoci. Kamar misalin Rotimi Amaechi, ya bada gudunmuwa sosai wajen kada Gwamnatin daya wuce.”
Bakare shine abokin takarar shugabancin kasa na Shugaba Buhari a shekarar 2011 a karkashin jam’iyyar CPC.
Title :
Tunde Bakare Ya Yabi Gwamnatin Buhari
Description : Babban Faston Cocin Latter Rain Assembly a jihar Legas, Fasto Tunde Bakare ya yabi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari akan nasarar data ke s...
Rating :
5