Tun dai bayan da shugaban majalisar wakilai a Najeriya, Yakubu Dogara ya raba shugabancin kwamitoci a zauren, wasu 'yan majalisar suke nuna rashin jin dadinsu da yadda aka raba kwamitocin har ma suke yin barazanar tsige shi.
'Yan majalisar wakilai daga jam'iyyar APC mai rinjaye dai su ne suka fi nuna adawa da yadda aka raba shugabancin kwamitocin.
Suna kuma zargin cewa mafi yawa daga kwamitocin masu gwabi-gwabi sun tafi ga 'yan adawa marasa rinjaye na jam'iyyar PDP a majalisar.
Garba Chede, dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Taraba ya shaida BBC cewa za su dauki matakai da ka iya kai wa ga a tsige kakakin nasu matukar bai sake fasalin rabon kwamitocin ba.
Sai dai kuma bangaren shugaban majalisar sun ce wannan zance marar tushe.
A ranar Litinin din nan ne ake saran kakakin majalisar wakilan na tarayya, Yakubu Dogara zai kaddamar da shugabannin kwamitocin Majalisar da mataimakansu.