sojojin Nigeria sun kawar da manyan sansanin Boko Haram Tara a jihar Borno
Rundunar Sojin Nigeria ta yi ikirarin cewa mayakan ta bataliya ta 28 sun samu gagarumar nasarar kawar da manyan sansanin yan kungiyar Boko Haram Tara dake yankin Lassa ta jihar Borno.
Kakakin rundunar sojin kasa ta Nigeria, Kanar Tukur Gusau, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a,
Yace sojoji sun kawar da sansanin yan Boko Haram dake garuruwan Lassa, da Muthavo, da Dagu Kumabza, da Isge, da Unworo Zangore, da Kilekasa da kuma Pumpum a wani farmaki da suka kai ranar 3 da 5 ga watan Nuwamba.
Yace sun kashe yan Boko Haram masu yawa, sannan sun kuma sami makamai da ababen hawa da mayakan suka gudu suka bari.
A gefe guda kuma a ranar Alhamis sojoji sun kai wani farmaki inda suka kawar da yan ta’addan a yankin Korede dake karamar hukumar Damboa .
Kanar Tukur yace sun gano babura Uku da ake zargin da su aka kai harin ranar Lahadi a kauyen Azir, da kuma shirgin kayan abinci da mayakan suka sace a kauyen.
Yace an kuma kawar da wani shingen yan ta’addan a garin Korode baya ga haka sojoji na daukar kwararan matakai a yankin garuruwan Azir, da Wajikoro, da Damboa da kuma Biu domin tabbatar da Boko Haram basu sake kai hari a yankunan ba.
Title :
Sojojin Nigeria sun kawar da manyan sansanin Boko Haram Tara a jihar Borno
Description : s ojojin Nigeria sun kawar da manyan sansanin Boko Haram Tara a jihar Borno Rundunar Sojin Nigeria ta yi ikirarin cewa mayakan ta bataliya ...
Rating :
5