Wata rana Sarki yana kilisa, sai ya tarad da wani dan kwikwiyo yana kwance, duk kiyashi sun cika bakinsa nishi ya ke yi dai dai, kansa. Ko yaya aka yi ya rabu da uwarsa, Allah kadai ya sani.
Da Sarki da dube shi sai tausayi ya kama shi, ya ja linzami ya tsaya, ya dubi mutanen da ke biye da shi, ya ce, “A, kakkabe wa Sarkin Babanni ya lura da shi da kyau yana ba shi abinci, in yana da sauran kwana gaba ya tashi.”
Nan da nan, kafin Sarki ya rufe baki, bayi sun dira sun kama karen, sun shafe masa baki da hannanyen rigunansu. Wani ya sa shi kan kwacciya, ya tafi da shi gida ya kai wa Sarkin Babanni, ya Sarki. Da rana ta yi sanyi suka komo.
Bayan kamar kwana uku sai dan kare ya farfade, har ya fara tafiya, Da ya sami kamar wata biyu sai ya zama kamar ba shi ba. Ya yi bulbul, duk inda Sarki za shi yana biye. Da ya girma sai kullum dare in Sarki ya shiga barci, shi kuwa sai ya zo kofar Saboda haka Sarki ya rika sonsa kwarai da gaske. Ba mai ikon ya buge shi, ko ya yi masa wata katuwar tsawa, don tsoron Sarki.
Ana nan, ran nan safiyar Salla Sarki ya yi shiri zai fito ya hau zuwa idi, sai karen nan ya biyo. Sarki ya waiwaya ya gan shi, ya buga masa tsawa, ya koma daki ya kwanta, don ya san haka a kan yi masa in ba a son ya bi.
Yana nan kwance dakin Sarki, can an kusa saukowa daga idi, sai aka kare toye-toyen Salla. Wata sadaka ta fara dauko kwano guda ta kawo cikin dakin nan ta aijye. Amma maimakon ta rufe abincin yadda ya kamata sai ta bar shi a bude, don ta san ko da zai rube karen nan ba shi tabawa.
Karen nan yana kwance, sai ya ga wani kumurci ya biyo matakin soro, ya sauko daga kan azara, ya sa baki cikin abincin yana ci. Kare ya fita wage yana haushi don mutane su zo. Ba wanda ya kula da shi.
Da mata suka ji ya dame su da hausahi, sai suka dauki dutse suna jifarsa, don sun ga Sarki ba ya nan. Da karen nan ya ga ba su gane abin da ya ke nufi ba, sai ka kyale ya shiga daki ya kwanta. Maciji kuma da ya ga ya koshi, sai ya sulale ya koma cikin azara abinsa ya shige.
Can an jima Sarki ya dawo. Da shigowarsa iyali suka yi masa barka da sauka. Bayan sun tashi, ya nufi wajen abincin nan zai ci. Kare ya bi shi yana kada wutsiya kamar ya ce, “Kada ka ci, maciji ya zuba dafi a ciki.” Allah bai ba shi ikon magana ba.
Sarki ya wanke hannu ya sa cikin abinci abinci, ya yanko. Kare kuwa sai ya kai nan ya kai na, Sarki na tsammanin son abinci ya ke yi. Ya jefa masa ya ki ci, sai haushi ya ke yi wa Sarki.
Sarki ya bude baki zai sa wannan lomar sa’an nan ya dauki sanda ya kore shi, sai karen ya yi farat ya buge hannun Sarki, loma ta fadi kasa. Sarki ya dunkula hannu ya shiga dimar kare, amma kare sai gurnani ya ke, bai kula ba. Ya sa baki ya cinye loman nan da ta fadi daga hannun Sarki, ya kuma hau wa sauran abincin duk ya cinye sarai. Tun Sarki na dukansa, har haushi ya kama shi, ya gaji ya bari. Ya tsaya kurum ya ga ikon Allah.
Ko da kare ya cinye abincin nan, sai ya koma gefe guda ya kwanta. Kafin Sarki ya kare ciccika, kare ya mimmike nan ya mutu.
Ganin wanan abu fa ya kara ta da hankalin Sarki, ya ce, “Lalle akwai wani abu game da abincin nan. Watakila sadakar da ta kawo ta yi mini sammu ne in ci in mutu.”
Sai sarki ya fito ya kira ta, ya tambaye ta, tarantse da abin da zai kasha ta ba ta sa kome ba ciki. Ya tantambayeta ko ta bari garin sauran kishiyoyin, ta ce a’a, da karewa sai ta zuba cikin wannan kwano ta kawo.
Sarki ya ce, “To, da kika fita ba wadda ta shigo bayanki?”
Sadaka ta ce, “Mts, bayana ba wadda ta shigo. Ba na daukan akhakin wani, ni kadai na dawo na bude, don ya sha iska da na ji kuna tafe.”