An karrama wasu daga cikin taurarin fina-finan Hausa da aka fi sani da 'Kannywood' a wani biki da aka gudanar da birnin London.
A bikin 'African Film Awards', fitaccen tauraron Kannywood, Ali Nuhu da Adam A Zango da kuma Hafizu Bello duk sun samu kyautuka.
Ali Nuhu wanda ke fitowa har ma a fina-finan Nollywood ya samu kyautar bajinta ta wanda aka dade ana damawa da shi.
A yayin da Adam A Zango, wanda shi ne tauraron fim din 'Gwasko' da aka fitar a bana, ya samu kyautar fitaccen tauraron fim.
Shi kuma Hafizu Yahaya an ba shi kyautar mai bada umurnin da ya fi kowanne a bana a fina-finan Kannywood.
An shafe shekaru 19, ana gudanar da bikin ba da kyauta ga jaruman fina-finan Najeriya na 'African Films Awards' a London, amma sai a bana aka bai wa jaruman fina-finai na Kannywood.
Title :
[Photos] An Karrama Ali Nuhu, Adam Zango Da Hafizu Bello A London
Description : An karrama wasu daga cikin taurarin fina-finan Hausa da aka fi sani da 'Kannywood' a wani biki da aka gudanar da birnin London. A b...
Rating :
5