Babban dan wasan Golden Eaglets ta Najeriya nan na wasan kasa da yan shekara 17, Victor Osimhen ya amince da yarjejeniyar Tottenham Hotspur.
Metro.co.uk ta bayyana cewa sashen Mauricio Pochettino ta jima tana bibiyar shi. Sannan yanzu sun cinma yarjejeniya da dan shekara 16 din,.
Osimhen yaci kwallaye 10 a wasan kungiyar kwallon kafa ta yan kasa da shekara 17 a cikin wasanni 7, wannan ne ya sanya shi ya zama wanda yafi kowa cin kwallaye a sashen wasannin a duniya.
Abokin wasan shi kuma shugaban yan wasan na Najeriya na kasa da shekar 17 din, Kelechi Nwakali, ya tafi zuwa Manchester City inda zaya hadu da Kelechi Iheanacho.
Amma tshon kocin su John Obuh, wanda ya jagorance su daga 2010-2013 ya bayyana cewa kada suyi saurin zuwa kasashen ketare.
A wata hira da yayi da Naij.com Sport a waya, ya bayyana cewa kamataye su dawo gida su kara fasaha su fita a yan kasa da shekara 20.
Yace: “Ina fatan baza suyi saurin zuwa kasashen ketare ba. Kamatey su dawo gida su cigaba da wasa har sai sun fita daga yan kasa da shekara 20.”