Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanar da ma'aikatun da ministocin da ya rantsar za su jagoranta.
Shugaban ya bukace su da su zagen-dantse wajen gudanar da ayyukan da aka basu, yana mai cewa 'yan Najeriya sun zuba ido su ga irin rawar da za su taka wajen ci gaban kasar.
Tsohon gwamnan jihar Lagos, Babatunde Raji Fashola shi aka nada ministan makamashi, ayyuka da kuma samar da gidaje a yayin da aka bai wa Kemi Adeosun, ma'aikatar kudi.
Abdurrahman Dambazau shi ne ministan harkokin cikin gida, a yayin da aka bai wa Mansur Dan-Ali ma'aikatar tsaro sai Adamu Adamu da aka nada a matsayin ministan Ilimi.
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi shi ne aka bai wa ma'aikatar sufuri sai kuma Mr Okechukwu Enelemah a matsayin ministan cinikayya da kasuwanci.Amina Mohammed ita aka bai wa ma'aikatar muhalli a yayin da Muhammed Bello ya zama ministan babban birnin tarayya, Abuja sai kuma Solomon Dalung ministan harkokin wasanni da matasa.
Cikakken jerin sabbin ministoci da ma'aikatunsu;
Chris Ngige - Ministan Kwadago da ingantuwan aiki
Kayode Fayemi- Ministan Harkokin Ma'adinai
Rotimi Amaechi - Ministan Sufuri
Babatunde Fashola - Ministan Makamashi, ayyuka da samar da gidaje
Abdulrahman Dambazau- Ministan harkokin cikin gida
Aisha Alhassan - Ministar harkokin mata
Ogbonaya Onu- Ministan Kimiyya da Fasaha
Kemi Adeosun - Ministar Kudi
Abubakar Malami - Ministan Shari'a
Sen Hadi Sirika - Karamin Ministan a harkokin zurga-zurgar jiragen sama
Barr. Adebayo Shittu - Ministan Sadawar
Suleiman Adamu - Ministan samar da ruwan sha
Solomon Dalong - Ministan Wasanni da harkokin Matasa
Ibe Kachikwu - Karamin Ministan harkokin Man Fetur
Osagie Ehanire - Karamin Ministan Lafiya
Audu Ogbeh - Ministan Ayyukan Gona
Udo Udo Udoma - Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa
Lai Mohammed - Ministan Yada Labarai
Amina Mohammed - Ministar Muhalli
Ibrahim Usman Jibril - Karamin Ministan Muhalli
Hajia Khadija Bukar Ibrahim - Karamar Ministar Harkokin Waje
Cladius Omoleye Daramola - Karamin Ministan Naija Delta
Prof Anthony Onwuka - Karamin Ministan Ilimi
Geoffrey Onyema - Ministan Harkokin Waje
Mansur Dan Ali - Ministan Tsaro
Barr James Ocholi - Karamin Ministan Kwadago
Zainab Ahmed - Karamar Ministar Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren kasa
Okechukwu Enelamah - Ministan Cinikayya da Kasuwanci da kuma Masana'antu
Muhammadu Bello - Ministan Abuja
Mustapha Baba Shehuri - Karamin Ministan Makamashi da Ayyuka
Aisha Abubakar - Karamar Ministar harkokin cinikayya
Heineken Lokpobiri - Karamin Ministan ayyukan gona
Adamu Adamu- Ministan Ilimi
Isaac Adewole- Ministan Lafiya
Abubakar Bawa Bwari - Karamin minista harkokin Ma'adinai
Pastor Usani Uguru - Ministan Naija Delta