Shugaban kasa Muhammadu Buhari na haramar korar wasu da ke rike da manyan mukaman gwamnati da ya hada da, shugaban ‘yan sandan Nijeriya , Solomon Arase, shugaban hukumar kula da kasuwannin hannun jari, Peter Obi, shugaban hukumar Alhazai ta kasa ABDULLAHI Muktar Muhammed da sauran makamantansu. Wannan ya biyo bayan tattara mukaman da gwamnatin shugaba Jonathan ta yi a 1 ga watan Afrilu zuwa 28 ga Mayun na shekarar 2015, kafin mika zuwan gwamnati mai ci ta shugaba Buhari. Wadannan nade-nade tsohon shugaba Jonathan, ya aiwatar da su ne a cikin watanni biyu ne bayan ya sha mummunan kaye a wajen abokin karawarsa Muhammadu Buhari a 28 ga mayun 2015.
Wannan ya faru ne sakamakon kira da Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Dabid Lawal ya yi ga dukkanin sakatarorin gwamnatin tarayya na dindindin a 18 ga satumbar 2015, da su gaggauta kawo masa jerin sunayen kacokan masu rike da manyan mukaman gwamnati daga 1 ga Afrilu zuwa 28 ga Mayun 2015. Sannan ya ba su wa’adi cewa ka da kowanne daga cikinsu ya wuce 30 ga watan Satumba 2015 ba tare da ya kawo nasa jerin sunayen ba.
‘Sakataren ya kara da cewa mafiya yawan manyan mukaman da gwamnatin da shude ta yi, ba akan ka’ida da cancanta ta aiwatar da su ba. Wannan dalili ne ya sanya shugaban kasa ya bayar da umarnin cewa dukkanin sabbin mukamai da gwamnatin da ta shude ta yi a dukkannin manyan ma’aikatun gwamnati da ya hada da (Farastatal, Agencies da Commissions) daga 1 ga Afrilu zuwa 28 ga Mayun wannan shekara a tabbata an bi diddigi don ware zare da abawa’ in ji shi.
kamar yadda aka sani ne, shugaba Jonathan, ya nada babban Sifektan ‘yan sanda na kasa, Arase ranar 21 ga Afrilun 2015, bayan cire tsohon shugaban ‘yan sandan da shugaban ya yi Suleiman Abba daga mukaminsa. A hannu guda kuma, tsohon gwamnan Ananbra Peter Obi, an nada shi a matsayin shugaban SEC a 27 ga Afrilun 2015, inda shi ma nasa takwaran Abdullahi Muktar Muhammed aka nada shi a matsayin shugaban hukumar Alhazai ta kasa a ranar 5 ga Mayun wannan shekara, aka kuma rantsar da su a 22 ga Mayun duk dai ta wannan shekara da muke ciki tare da wasu manbobi da suka hada da: Yusif Adebayo Ibrahim, Abdullahi Modibbo Saleh, Ibrahim Azeani, Adeyemi Ademola Fuad, Enenwaryn Zikey, Aisha Maidubu Mohammed, Danjuma Salihu Usman da kuma Hajiya Ramatu Bala Usman.
Bayan faduwa zabe da shugaba Jonathan din dai ya yi, ya sake nada tsohuwar Ministarsa ta gona da raya birane, Madam Asabe, a matsayin sakatariyar asusun gudanuwar hada-hadar man fetir (Petroleum Ekualisation Fund), ta maye gurbin Mista Sharon Adefunke, Kasali bayan korarsa daga ofis da shugaban ya yi. Kazalika, malam Habib Abdullahi, inda shi ma aka yi awon gaba da shi Alhaji SANUSi Ado Bayero ya gaje shi daga kujerarsa ta daraktan hukumar jiragen ruwa ta kasa (Nijerian Port Authority).
Haka zalika, a hukumar kula da kasuwannin hannayen jari (SEC), Mournir Gwarzo, wanda ya jima yana rike da mukamin rikon kwarya tun bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar Arunmah Oteh a 2014 na shekarar da ta gabata, daga nan shugaba Jonathan ya tabbatar da shi a matsayin babban darakta mai kula da hukumar. Babu shakka rahotanni sun tabbatar da cewa, daga watan Afrilu zuwa Mayun wennan shekara, tsohon shugaban kasa ya nada Mista Olufemi A. Akinbade a matsayin sakatare na hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), bayan sauke dakta Femi Thomas a kan mukamin.
A takaicen takaitawa dai, kafin tsohon shugaba Jonathan ya bar ragamar mulkin wannan kasa a 29 ga Mayun 2015, ya nada sarakunan gargajiya a matsayin shuwagabannin jami’o’i 38 da muke da su a kasar nan. Haka nan awonni kadan kafin barin ofis, ya sake nada Alhaji Haruna Sambo da Mista Babatunde Igun a matsayin manyan daraktan bankin gona na kasa, a 28 ga Mayun 2015, amma a jikin takardar mukamin nasu aka rubuta 27 ga Mayu na 2015.
Kamar yadda muka samu rahoto daga fadar shugaban kasa cewa, sakataren gwamnatin Nijeriya Injiniya Babachir Dabid Lawal, tuni ya rantsar da kwamatin zai yi wannan aiki na hukumomin gwamnati. kazalika, sakataren ne zai shugabanci kwamitin, tare da Alhaji Mai Mala Buni, Ahaji Zakari Idde, Alhaji Inuwa Abdulkadir, Cif Pious Akinyelure, Cif Emmanuel Eneukwa a matsayin mambobi, inda Mista Gideon Sammani zai kasance a matsayin sakare.
Title :
Masu Gudu Su Gudu: Buhari Zai Tsige Manyan Jami’an Gwamnati
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari na haramar korar wasu da ke rike da manyan mukaman gwamnati da ya hada da, shugaban ‘yan sandan Nijeriya , So...
Rating :
5