Menene Annabina Macecina yai maka zaka zageshi????
* Ya bayar da jikinsa da ransa fansa dominka.. An zageshi, An chuceshi. an jefeshi da duwatsu amma duk ya jure domin kwadayin isar da rahamar Allah zuwa gareka.
Aranar Badar ya jure tsananin zafin rana da yunwa. Aranar Uhudu kuwa an harbeshi da kibiya, an sareshi da takobi, ya zubar da Jininsa. Amma duk ya jure domin tausayin al'ummarsa.
Aranar Khandaq an zagaye garinsa domin chutar dashi. Amma duk ya jure dominka.
Anyi masa Sammu, anyi masa Sihiri har tsawon kwana Arba'in amma ya jure duk akan hanyar nema maka rahamar Ubangiji. SHIN DON WANNAN KAKE ZAGINSA!!!
Aranar Isra'i da Mi'iraji ya kusanta da Ubangijinsa ya gana dashi. Awannan wajen ma bai manta dakai ba... Ya ambaceka ya nema maka alfarma awajen Mahaliccinka.. SHIN DON WANNAN KAKE ZAGINSA???
Aranar fitan ransa, bai gushe yana nema maka ceto da alfarma ba, har sai da ransa ya fita (saww)!!!
SHIN DON WANNAN KAKE AIBANTASHI, KO AIBANTA MAHAIFAN DA SUKA HAIFESHI???
TSINUWAR ALLAH TA TABBATA GA DUK WANDA YA CHUTAR DA MANZON ALLAH (SAWW) DA WANDA YA DAUKI NAUYIN ABUN, DA WANDA YAYI FARIN CIKI DA ABUN, DA WANDA YAQI DAUKAR MATAKI AKAN ABUN, DA WANDA YAJI HAUSHIN MASU YIN MAGANA AKAN ABUN.
BILLAHIL AZEEM bamu da komai bamu da kowa sai Allah da Manzonsa!!! Bamu san Allah ba, Annabinsa ne ya sanshi. Ta wajensa muke sanin Allah. Don haka duk wanda ya chutar dashi ya chuchemu!!
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.