Wata rana wani malami daga gabas da ya ji labarin Shaihu sai ya yiwo wa Sakkwato tsinke, ya zo ya ga abin da a ke fadi da idanunsa, domin an ce gani ya kau da ji. Da ya kusa da Sakkwato ya yi shiri irin na alhazai, ya shiga kokuwa, ya tafi wajen Shaihu Mujaddadi, ya ce, “Ina da fatawa, ya Shugabana.”
Shaihu dan Hodiyo ya amsa, “Allah ya sanasshe mu!” Mutumin nan ya ce, ‘Ya Shugabana, da me a ke miya a nan kasarku?”
Shaihu ya ce, “Da kuka, da gishiri, da tosshi, da daddawa.”
Mutumin nan ya ce, “To, ashe sun sha bamban da na kasarmu.” Ya yi ban kwana da Shaihu, ya fita. Shaihu ya ci gaba da sha’anin da ya ke ciki na jihadi. Aka ci kasashe, aka ba wadansu tutoci, sai can bayan shekara biyu har an manta da wannan mutum da ya yi tambaya, sai mutumin nan ya dawo, ya sami irin kayan Hausawa, ya yi shiri yadda ba mai ganewa shi ya zo bara waccan. Ya tafi wajen Shaihu ya gaishe shi, ya c,e “Da me kuma?”
Da ya ke Shaihu dan Hodiyo a;’amarin nasa ya yi nisa, ya tuna tambayar bara. Ya dubi mutumin nan, ya ce, “Idan da wadata a kan sa nama.”
Ko da bakon nan ya ji haka, sai ya fadi ya nemi Shaihu dan Hodiyo gafara, ya sallame shi ya koma garinsu.
“Tsakaninka da Allah, Allah ya ba ka nasara, ka taba jin wannan irin labari na Shaihu Mujaddadi in ba yau ba?”
Musa ya ce, “Gaskiya dai, ban taba ji ba. Shin don Allah ko kai ka kaga shi yanzu?”
Aku ha kada kai, ya ce, ‘Haba, Allah ya ba ka nasara, wallahi ba yanzu na kera ta ba, ni ma haka na ji shi. Ko mutum na hauka, irin karairayin nan da a ke wa tatsuniyoyi a yi wa tarihi kamar na Shaihu Mujaddi dan Hodiyo? Haba, a wargi wuri ya ke yi.”
Musa ya ce, ‘To, ko da ya ke haka, kana tsammani wannan ya fi wanda na gaya maka jiya ban mamaki?”
Aku ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai ba gardama na ke ja da kai ba. Wadannan al’amura ne na waliyyai, idan aka yi zurfi ciki, sai a tasam ma yin aabo. Ba mu da wata ta cewa, sai Allah ya ba mu albarkacinsu, amin, amin, amin!”
Musa ya ce, “Gaskiya ne, Allah dai ya kiyashe mu azabobin Jumma’ar da ba ta da Asabar, domin alfarmar Shugaban talikai!” Ya juya zai tafi.
Aku ya ce, “Af, Allah ya ba ka nasara kana ya sami me?”
Musa ya waiwayo, ya ce, “Kana ya sami me fa?”
Musa ya ce, “Me ka ke nufi da Kana ya sami ne?” Wa ka ke maganarsa? Wane abu zai samu? In kana tambayar wani abu ne ka fadi mu ji. Kai ba abin da ke dibarka sai samartaka. To, ni na aske.”
Aku ya duka, ya ce, “Allah ya huci zuciyarka, yallabai, Sairam ta,bauar da ma uo ,ala jiya, da na so in gani in ka iya lyad da jawabin da ka fara ba ni, don ka ce tarihin da na bayar yanzu na Shaihu Mujaddadi ba shi ba bam mamaki kamar wanda ka bayar jiya.”
Musa ya ce, “wane tambaya ka yi mini jiya?”
Aku ya bushe da dariya, ya ce, “jiya-jiya har ka manta, rankaya dade? Na tambaye ka shin sai mutum ya sa me da me a jikinsa za a san lalle ya yi ado, ba kushewa To, ina ga wannanda aka yi da shekara biyu?