Kotun sauraron karrakin zabe ta jihar Taraba ta bada umarnin rantsar da Hajiya Aisha Jummai Alhassan a matsayin gwamnar jihar ba tare da bata lokaci ba.
Alkalin kotun Justice Musa Danladi ya bada umarnin yayin da yake yanke hukunci akan karar da Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta jam'iyyar APC ta shigar inda ta kalubalanci zaben da aka yiwa Darius Ishaku na Jam'iyyar PDP.
Kotun ta ce jam'iyyar PDP ba ta gudanar da cikakken zaben fidda gwani ba kafin ta tsayar da dan takararta Darius Ishaku wanda hukumar zabe INEC ta baiyana a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
Title :
Kotu Ta Soke Zaben Jihar Taraba.
Description : Kotun sauraron karrakin zabe ta jihar Taraba ta bada umarnin rantsar da Hajiya Aisha Jummai Alhassan a matsayin gwamnar jihar ba tare da bat...
Rating :
5