Ya had'e cikin farar shadda tasha surfani. Yana kokarin dora hularsa ne idonsa yakai kanta ta madubi. Tana kwance abinta akan gado da tsohon ciki,daga ita sai riga da wando na bacci kan ko d'ankwali babu sai kyalli yake sakamakon relaxer daya takura mata sukaje da Bahijja aka sanya musu. Kallonsa kawai takeyi babu abunda ke yawo a idanuwanta sai zallar tsananin so da kaunarsa. Murmushi yayi ya d'aga mata gira
"Kallon nan fa?"
Ta kauda idonta tana basarwa ta hanyar zuro kafafuwanta k'asa da mik'ewa tsaye
"Uh uh,ina laifi a ciki don na kalli mijina? Kyau kayimin."
Yayi dariya yana mai janyota jikinsa
"Zan tafi masallaci,bayanaddu'ar haihuwa lafiya,wacce kuma kike bukata?"
Ta tureshi kad'an tana turo baki
"Kishiya."
Haka kawai yaji gabanshi ya fad'i ba tare da yasan dalili ba. Ya dad'a janyota yana murmushi
"Ita kike so?"
Ta harareshi
"Itace banaso kuma kaima shaida ne."
Ya shak'i k'amshi gashinta yana mai lumshe ido
"Bari fargaba Siyama,banda ra'ayin ajiye mata biyu kinji ko?"
Tayi murmushi tana mai sauke ajiyar zuciya,ita kanta tasan Allah Ya d'ora mata son Jafar sosai. Ganin yana kokarin fad'awa wata jahar tayi saurin tureshi
"Kai kam bansan sunanka ba,ka fiye takura mutum. Zaka makara fa."
Yayi saurin duba agogo,ya ja karamin tsaki
"Kinga kuwa na kusa."
Ya d'ora hularsa ta zauna daram,wayoyinsabiyu,da karamar Nokia da BB ya sanya a aljihunsa. Ya dubeta
"Shikenan,sai an sauko."
Ta gyada kanta yayi gaba domin kuwa tun zuwan Bahijja ya bar tafiya da mukullinsa acewarsa kada ta sanya ido takai maganar gidansu ya zama tsegumi.
**********
Daga masallaci Jafar gidansu ya soma zuwa. Wajensu Siyama ya fara shiga. Hajiyar Siyama da ma aikatan gidan sunyi kace kace suna aikin sallah. Yayi sallama ya shigo. Kallo d'aya tayi mishi ta had'e fuska don daman tunda taji labarin Bahijja tana wajen Siyama ranta ke a b'ace a cewarta don me Siyama bata fad'a mata tana neman mataimakiya ba. Haka tayi kiran Siyama ta bud'e mata wuta,har da fad'in matukar bazata fita harkar gidansu Jafar ba wadanda sam ba kaunarta sukeyi ba toh lallai kuwa tana tare da wahala. Siyama ko Jafar bata fad'awa ba gudun kada ransa ya b'aci.
Ya durkusa ya gaisheta,ta amsa dakyar. Ya cigaba da yi mata fatan alheri na kammala azumi lafiya amma tayi burus dashi. Ganin haka ya mike yana amsa gaisuwar ma aikatan kafin ya juya ya shige sashen Abba.
Abba yana zaune yana amsa waya,shima yaci adonsa na idi,babbar rigarsa tana ajiye a gefe. Jafar yayi sallama ya shiga,saida Abba ya ajiye wayar sannan ya dubeshi fuska a sake.
Bayan gaisuwa ya tambayi lafiyar iyalinsa,Jafar ya amsa mishi da kowa lafiya. Abba ya jinjina kansa
"Ina fatan babu wata matsala?"
Jafar yayi saurin amsawa
"A'a Abba,komai Alhamdulillah."
"Toh Masha Allah,sai a cigaba da hakuri. Allah Yayi maku albarka."
Yaji dadin addu ar ya amsa da amin,sun jima suna hira kafin Jafar yayi masa sallama ya fita zuwa gidansu.
Yana kwance akan kujerar Hajja ne wayarsa tayi k'ara. Ya janyota ya duba. Lambar Hadiyya ce kamar yanda yayi saving. Ya manta rabon ma da ya tsinci sak'onta a wayarsa,ya manta da lamarinta gaba d'aya. Kamar bazai amsa ba saidai ya danna yana mai karawa a kunnensa
"Assalamu alaikum."
Ya fad'a cikin sanyin murya,ta amsa da nata muryar data kere nashi a sanyi da kuma dad'i.
"Wa alaikassalam,barka da sallah Abokina. Anyi sallah lafiya?"
"Aboki?" Ya nanata a zuciyarsa,saimata bashi dariya,yayi murmushi
"Alhamdulillah,saidai ni sunana Jafar not Aboki."
Tayi 'yar dariya
"Madallah da wannan daddad'an sunan. Ina fatan ban matsawa rayuwar yaya jafar ba?"
Haka kawai yaji ta burgeshi,yayi murmushi karo na ba adadi
"Kin kusa dai Hadiyya. Kema ina fatan kinyi sallah lafiya?"
Ta marairaice murya
"Ka sanyayamin jikina yaya jafar,kayi hakuri don Allah. Wallahi hakanan naji kawai jinina ya hadu dakai a tun ranar dana soma jin muryarka."
Ya girgiza kai kamar tana ganinshi
"No,is ok. Kada ki damu kanki ai mutum rahma ne. Nagode ki gaidamin 'yan gidan naku saida anjima."
Yayi saurin katsewa,daidai lokacin Hajja ta shigo dauke da kulolin abinci yayi saurin karb'ar mata ya ajiye.
"Ikon Allah,daman kazo ne?"
"Na shigo Hajja,naga kuna aiki ne shiyasa na zauna na d'an huta."
Ya gaisheta,suka d'an tab'a hira kafin ya wuce wajen Mahaifinsa. Nan ma ya jima sannan yayi musu sallama ya tafi.
Lafiyayyun girke girke ya tarar,yasan aikin Bahijja ne. Siyama itama anci kwalliyar sallah. Bahijjah ta gaisheshi ya amsa mata,sannan ta basu waje ta koma domin cigaba da tattare kicin d'in......!
****
Bayan sallah da sati d'aya,tuni Bahijja ta koma gidansu saboda makaranta. Aka sake komawa gidan jiya tsakanin Jafar da Siyama. Hakuri kawai yakeyi da ita,abun nata tun yana ganin har da ciki har dai ya gane sabon lalaci ne kawai ya ziyarceta. Domin sadda Bahijja tana nan babu abunda bata sakar mata ba,har wankin undies dinta,abunda yafi tsayawa a ran Bahijja kenan. Toh da babu ita wanene mai wankewar? Jafar, zuciyarta ta amsa mata,tausayin yayanta fal a zuciyarta haka ta bar gidan.
Jafar ya koma gyaran d'akinsa da kanshi,karshe ma saboda haushi ya hanata shigar masa d'aki. Hakan ya k'ona ranta matuk'a
"Yanzu ni kake kora my j?"
Ya d'aure fuskarsa tam,fushine wanda bata tab'a ganin irinsa tattare dashi ba. Ya k'ara nuna mata hanyar waje
"Bazan iya had'a gado dake ba Siyama,na gaji da kwana dake kina tashin k'arnin da banaso. Matuk'ar bazaki bar ciye ciyen kifi ba a gidannan lallai bazamu shirya ba. Don haka tunda kin tabbatar min bazaki iya gyara jikinki kafin had'a jiki dani ba,saiki ficemin a d'aki ki koma naki d'akin."
Siyama ta fashe da kuka,a fusace tace
"Nagode Jafar! Daman nasan ba don Allah kake sona ba sha'awata kakeyi. Duk kokarina baka gani? Ga nauyin ciki ga fama da aikace aikacen gida duk baka gani ba? Ni bazan iya wanka sau biyu ba! Idan bazaka kwanta dani a hakan ba shikenan!"
Fuu! Tayi waje tana kuka,yaja tsaki ya furzar da iska cike da takaicin Siyama. Ko kad'an furucinta baisa ya tausayamata ba. Ya kakkab'e gadonsa ya rufe k'ofa,har ya kwanta ya mike yana tsaki. Turaren wuta ya kunna ya bud'e tagogin d'akin bayan ya ware fanka. Sai lokacin ya iya kwanciya zuciyarsa fal da tunanin irin wannan rayuwa tasu. Anya zai iya cigaba da rayuwa haka? Mtsw. Yaja tsaki karo na biyu,dakyar bacci ya daukeshi.
Ita kuwa Siyama ranta idan yayi dubu toh ya b'aci,ashe dagaske ne wasu mazan basu da mutunci? Ita Jafar yake wulakantawa kawai saboda tana dauke da cikinsa? Ta janyo rigarta tana shinshinawa,yanzu duk da uban turaren data fesa amma yace yaji k'arni? Toh wai ya zatayi? Ta saba ko a gida bata da abincin da tafi so kamar kifi. Ai kuwa saidai su zuba tasan ma bazai jure ba. Ta sauke kayayyakin dake kan gadon,ta kwanta batare data damu da kakkab'ewa ba ballantana kuma addu'a...
********
Shak'uwa ta fara neman shiga tsakanin Jafar da Hadiyya. Har ya zamana Jafar kan d'auki wayarsa yayi kiranta idan yaji shiru kwana biyu. Yanason hira da ita, tasan abunda ya dace ta fad'a tasan wanda bai kamata ba. Hakanan akwai ta da barkwanci wannan tasa sau da yawa idan Siyama ta b'ata ransa yakan mance idan yana tare da ita.
Akwai sadda Haris ya iskeshi a shagonsu yana waya yana tuntsirar dariya. Ya zuba masa ido har ya kammala,ya lura da mace yake wayar. Jafar ya dubeshi yana harararshi
"Menene kuma kakemin wannan kallon?"
Haris bai bar kallon nashi ba ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi
"Ina kallon sabuwar soyayya ne."
Jafar ya ja tsaki,ibrahim dake jera atamfofi ya hau dariya.
"Kaima dai ka kula kenan Haris,ni ai dayake ya rainan wayo k'aryatani yayi da cewar yar uwarsa ce."
Jafar ya girgiza kanshi yana tab'e baki
"Kudai kam banda sa ido baku ajiye komai ba. Hadiyya tamkar kanwata na dauketa. Wani abu?"
Sukayi dariya,Haris yace
"Babu komai kam,ai daman da haka da haka ko ya kace Ibrahim?"
Ibrahim dariya kawai yake yana kallonsu. Jafar ya daki cinyarsa
"Banason sharri,yarinyartana da hankali. Garin neman layin wani yayanta ne muka had'u ta waya shine muke gaisawa amma kun kama kuna juya magana. Taso kayimin rakiya."
Suna dariya Haris yana fad'in
"Ahaf,ai na fadamaka daga haka daga haka za'aji sabuwar magana,'yar ina ce?"
Ya d'aga kafad'a bayan ya mik'e tsaye
"Ina na sani? Ban tambayeta komai nata ba."
Suka kama tafiya,Haris yace
"Wai ina zamuje? Nifa na kusa komawa ofis kafin Baffa ya bincika yaji bana nan ya hau fad'a."
"Yunwa nakeji,yau dai saika d'and'ana girkin shagonsu mama da nake yawan baka labari."
Haris ya zaro ido
"Au,wai kai har ila yau baka bar zuwa ba?"
Jafar cike da damuwa yace
"Ta yaya zan bari bayan waccan kazamar gidan bata chanja ba? Nikam abubuwanta sun isheni. Kana gani fa hatta anti tazo takanas tayi mata fada da nasihu amma a banza. Haka akeso na zauna na k'are rayuwata?"
Haris yace
"Tab! Toh Allah Ya kyauta. Siyama kuma sai addu'a abun yayi tsamari."
"Barta ta cigaba dai,zanyi maganinta matukar bata gyara ba."
Haris ya kalleshi. "Me zakayi?"
Jafar yayi mishi wani irin kallo kafin yayi murmushi,Haris tuni ya d'ago zancen,ya nunashi da yatsa
"Kasan Allah ka rufawa kanka asiri,baka ganin yanda na rame kwana biyu? Aure ba abune mai sauki ba,yanzu haka ma baro ummina cikin fushi. Gaba daya ta tashi hankalinta,musamman ganin yanda akayi gyara gyaran gida,sai ta hau fad'an wai meyasa banyi ba tun a baya saida zan k'ara aure? Hakanan dole saida ta sanyani a gaba na kaita taga gidan Rahma taga baifi nata komai ba sannan hankalinta ya d'an kwanta. Toh yau da safe kuma ganin katunan daurin aure duk saita hargitsemin. Zaman ofis ne ya gagareni shiyasa ka ganni anan. Banason bacin ran Ummina ko kusa,ji nakeyi tamkar na fasa auren nan saidai inason Rahma sosai."
Jafar yayi dariya ya girgiza kai
"Allah Sarki,maza muna hakuri. Ta ko'ina ba sauki saita Allah. Kayi hakuri fa,na tabbata zafin kishi ne don kanta zata zo ta sauko. Kaidai ka dunga kokarin kwatanta adalci domin Allah. Ai Ummi akwai hankali,na tabbata yanzun ma kishi ne kawai amma ka d'an bata lokaci."
Ya jinjina kansa daidai lokacin da suka iso shagon. Ta hangoshi batasan lokacin data saki ajiyar zuciya mai k'arfi ba had'e da murmushi musamman ma idan ta tuno da yanda yake hira da ita a yanzu sosai ta waya. Suka zauna bayan sunyi sallama. Mama tana dariya tace
"Ikon Allah,yau dai kaine mutum na farkon soma ziyartar shagon nan cin abincin rana Jafar. Barkanku da zuwa."
Suka dubi juna shi da Haris sukayi murmushi. Haris yana mamakin yanda har suka saba da amininsa har haka.
Ladi ta nufosu a nutse,ta durkusa ta gaishesu murmushi yak'i yankewa akan fuskarta. Suka amsa ta nemi sanin abunda suke buk'ata Jafar ya harareta cikin wasa.
"Yau kuma sai an tambayeni?"
Tayi dariya
"Lah yayana ai gani nayi kaida bak'o....."
"Wannan aminina ne Haris sunansa. Ba bak'o bane saidai ba'a nan kasuwa yake zaune ba."
Ta k'ara duban Haris wanda ke k'are mata kallo tayi murmushi
"Ayya,barka da zuwa yaya haris, kai kuma me za'a kawo maka?"
Ya girgiza kansa zaiyi magana,Jafar ya tareshi da sauri.
"Kawo mishi tuwon shima."
Bayan tayi gaba,Haris ya harareshi
"Kanason k'ara jawomin fitina kenan ko? Ban koma gida ba nasan dole Ummina ta nemi sanin inda naci abinci."
Jafar yayi dariya
"Yau fa d'aya Haris, so nakeyi ka d'and'ana girkin mutanen nan wallahi akwai dad'i sannan komai nasu a tsaftace. Ji yanda wajen ke tashin k'amshi kamar ba'a kasuwa ba."
Haris ya gaskata tsaftarsu da idonsa,kafin ya k'ara duban Jafar
"Amma buzaye ne ko? Sunyi kama da buzaye wallahi musamman Maman,naga ita bak'a ce d'iyar."
Kafin Jafar ya bashi amsa, ta dawo dauke da kwanuka,ta ajiye ta dauko wasu ta k'ara ajiyewa gaban Jafar,sannan ta ajiye musu ruwa da lemo mai sanyi dana wanke hannuwa kafin ta juya ta koma bakin aikinta. Duk rabin hankalinta yana ga Jafar sai murmushi takeyi.
Sai lokacin Jafar ya bashi amsarsa
"Buzaye ne mana,'yan nijar ne saidai mahaifinta ne d'an garin nan shi kuma ya rasu. Shine suke cigaba da rayuwarsu anan."
Haris ya jinjina kanshi kawai saboda dad'in abincin daya soma fusgarshi.
Mama ta tab'ata,a firgice ta dubeta
"Wai bazaki raba kanki da tunanin Jafar ba? Sai kije ki sallami wadancan(tayi mata nuni da wadanda suka shigo)
Ladi tayi farr da ido,ta sauke ajiyar zuciya. Jafar yana neman kasheta da salon gayunshi. Ta taka a sanyaye zuwa wajen mutanen da suka shigo.
Koda su Jafar suka kammala suka fito,santi kawai Haris ke zubawa. Yana yabon girkin.
"Wannan bashi da bambanci dana Ummina,gaskiya sun iya abinci lafiyayye."
Jafar yana jinsa har ya rakashi wajen motarsa. Banda murmushi babu abunda yakeyi saidai baice komai ba. Bayan Haris ya shiga ya zauna ne ya dubi Jafar cike da tsokana yace
"Kodai da ita zamuyi ta biyu ne?"
Yaja tsaki ya harareshi
"Amma dai kaima sai a barka,so kakeyi na zama abin nuni a kasuwa. Mijin mai abinci ko? Bata burgeni bazan iya aurenta ba."
Ya k'arashe yana juya kansa, Haris yayi dariya
"A'a fa,kada azo..."
"Sai munyi waya. Dan iska kawai."
Yana fad'in haka ya bar wajen suna yiwa juna dariya. Jafar abun ma dariya ya bashi,me zaiyi da Ladi yana da kamar Siyama? Ai koda zaiyi aure bazai auri irinsu Ladi ba da suke yini cikin kasuwa...
Xama yay maganane..
Mude je xuwa..!