Cikin ikon Allah,rayuwa tana tafiya har aka shiga watan azumin Ramadan. Lokacin watannin cikin Siyama hud'u da kwanaki.
Alokacin Siyama ta k'ara zama malalaciya,batason yin aikin komai kullum cikin bacci take. Ta k'ara k'iba abinta. Jafar kam hankalinsa ya karkata sosai wajen kula da ita,baya takura mata akan aiki. Hakanan yake lallab'awa suna ragewa tare da Dauda. K'arshe ma ganin an yiwa kannensa hutu ya nemi alfarma,Hajja tace sam,dakyar dai, da kuma sanya bakin Alhajinsu ne, Hajja ta bashi damar tafiya da Bahijja. A hanya suna tafe a mashin ya dubi Bahijja ta gilashi fuskarsa a daure
"Saura kuma kiyi recording abubuwan da zaki tarar ki barbazamin sirrin gida. Ki iya bakinki."
Bahijja dariya taso kubce mata,toh wai wanene ya gayamishi ma basusan Anti Siyama KAZAMAR GIDA ce ba? Tun kafin auren babu abunda basu sani ba tare dasu Husna don ko rannan taji Hajja tana mita bayan taje gidan. Lallai ma Jafar baisan kazantar Siyama ta gama cika danginsu ba.
Hankalin Bahijja ya tashi kwarai ganin yanda gidan ya koma wai ma a hakan don Jafar yana tattarawa. Tana yamutsa fuska har ta soma kyankyami,anya zata iya sati biyun nan kamar yanda Hajja ta fad'a? Jafar ya dubeta gira a had'e
"K'araso ciki kin tsaya kina kalle kalle."
Ta shiga da sauri. Siyama tana kwance tana amsa wayar yayarta rumaisa. Batun wani biki sukeyi daya danganci can dangin Hajiyarsu da za'a gudanar bayan sallah. Da murnarta ta tarbi Bahijja.
"Ina su Hajja? Yau kifin ruwa kece kika yarda zakizo gidana? Lallai my J kayi kokari."
Bahijja sai yak'e takeyi,tamkar ta mik'e ta rufeta da duka takeji. Ita kanta Siyamar a hargitse take,ko ita da bata da kyawun fuska ta fita tsaf tsaf. Jafar ya mike
"Ai Hajja tana tausayamaki ne,kinga ga azumi ya nufomu ga ciki hidimar sai tayi maki yawa."
Ya dubi Bahijja
"Shiga ki ajiye kayanki ki fito ki hau gyara. Ni zan koma kasuwa."
Bahijja ta mik'e
"Yaya a dawo lafiya."
Tayi jim ta gani ko Siyama zatace wani abu koda addu'ar ne amma ina,saima tambayar data jefowa Bahijja.
"Allah Yasa Hajja ta baki gasarar tawa."
Bata ce mata uffan ba tayi d'aki,gadon a gyara yake,hakanan d'akin a share. Ta tabbatar da wuya idan ba Jafar ne yayi ba.
Haka Bahijja tayi zaman bauta a gidan,sannan iyakacin kwanakin da tayi ta gama jin kaunar Siyama ta sire a ranta. Banda ma jininta ce babu yanda zatayi da ko hanyar da take bi bazata kalla ba. Ta gama k'uluwa a lokacin da azumi yakai sati biyu cif amma Jafar ya hanata tafiya ko'ina yace ya sanarwa Alhajinsu cewar bazata koma ba sai bayan azumi. Wayyo! Tamkar Bahijja ta d'ora hannu akanta. Babban abunda yafi bata bakin ciki idan an ajiye kazantar Siyama gefe bai wuce yanda ko kusa bata kula da girki da komai na mijinta ba amma an iya idan ya dawo ayita nad'ewa a jikinshi kamar mage ko kunyar Bahijja bataji. Batasan amfanin karatun littafi ba ga wasu mutanen! Daga mazan har matan mafi yawansu sunfi mayarda hankulansu ga nishad'in dake a littafin ba wai darusussukansa ba! Ina amfanin mace mai bin bokaye tana daukar littattafan hausa ta karanta amma bata daukar darasi ko d'aya? Ina amfanin maza masu wulakanta matansu sannan suna karatu amma komai baya shiga kwakwalwarsu na darasi. Meye amfanin karatun da akeyi ba a koyi da darussan cikinsa?
Ta girgiza kanta cike da bakin ciki lokacin da ta janyo littafin da Siyama ke karantawa a yanzu,ZURFIN CIKI.
Tsaki taja,Allah wadaran wasu matan. Tabbas Siyama tana bukatar gyara sosai a rayuwarta a sanin da tayi cewar yayanta fa d'an kwalisa ne tun yana gidansu. Tana jiye mata tsoron kada watarana ya gaji. Ta tab'e baki ta maida littafin mazauninshi ta cigaba da jan casbaha tana salati....!
******
Ladi tana tsaye,Mama tana yi mata gargad'in kada ta fita yanzu zasu je su dawo daga dubiyar wata makwafciyarsu da yaronta ya k'one a asibiti.
"Yanzu zan dawo ki tabbatar kin rufe..."
"Wai Binta kodai muyi gaba ne?"
Muryar makwafciyarsu Harira ya katse Mama. Tayi saurin ficewa Ladi na yi musu addu'ar dawowa lafiya. Bayan sunyi nisa,ta dawo da saurinta ta rufe k'ofar. Cikin d'oki ta bud'e jakar makarantarta ta fiddo katin mtn da take faman ajiyarsa kusan sati biyu da kwanaki kenan da niyyar kiran Jafar. Sai yau ta samu damar.
Bayan ta tabbatar da katin ya shiga ne,ta lalubo lambar Jafar ta danna kira. Lokacin k'arfe hud'u na yamma,ta tabbatar yana kasuwa. Kasancewar azumi ne,basa fita sai bayan la'asar hakanan sun d'aukarwa kansu hutun shiga kasuwa ranar Alhamis da juma'a don su samu dama sosai na yin ibadarsu. Jafar kuma rabonta dashi tun kafin azumi.
Wayar tayi ta ringing ba'a dauka ba har ta katse. Cikin damuwa ta soma kok'arin k'ara danna kira sai kuma gashi ya biyo baya. Saida taji fad'uwar gaba,dakyar ta iya d'auka.
"Salamun alaikum."
Ta amsa cikin siririyar murya. Ta k'ara da cewa
"Yayana barkanka da yammaci,ya azumi ya kasuwar?"
Jafar dake tsaye yana k'ok'arin fiddowa wasu 'yan mata material ya amsa
"Yauwa barka dai,mun gode Allah. Saidai ban gane me maganar ba."
Tayi dariya cikin wasa tace
"Hadiyya ce."
Jafar dayake hankalinsa yana ga aikinsa,yace
"Banganeki ba,amma ki bani mintuna ina zuwa."
Ya ajiye wayar suka cigaba da maganar kud'i da yan matan,sun jima suna bugawa k'arshe ya hak'ura ya siyar musu a farashi mai sauki sauki. Saida ya sallamesu ne,ya zauna ya d'auki wayarsa,lambar ya gama k'arewa lambar kallo
"Hadiyya?"
Mamaki yakeyi,toh wacece kuma Hadiyya? A ina ta samu lambarsa? Ya tab'e baki ya k'ara danna kiranta kamar yanda yace mata.
Ladi dake zaune tana duban wayarta,tuni zuciyarta ta kissima mata wata shawara,murmushi kawai takeyi tana mai fatan Allah Ya bata nasara ta ida nufinta na alheri. Kwatsam kiransa ya k'ara shigowa,tayi saurin d'auka. Bayan sallama Jafar ya sake maimaita tambayarsa cikin muryarsa tausassa
"Malama Hadiyya,ko zan iya sanin wacece ke? A ina kika samu lambata?"
Ladi ta k'ara kwantar da muryarta
"Ba lambar yayana Abdullahi bane?"
Ya girgiza kanshi tamkar tana ganinshi
"No,bashi bane. Am sorry,wrong number kikayi dialing."
"Ayya,bakomai nagode."
Bayan sun ajiye wayar ne,ta tsaya tsam tana kallon wayar,kwallah ta cika idonta. Anya hanyar da take shirin bi zata b'ullar da ita? Ko zata tura masa sak'o ta sanar dashi cewar Hadiyya itace Ladi? Zuciyarta sai k'arfafa mata gwuiwar yin hakan takeyi,saidai kuma bata da kuzarin aikata hakan tafi kaunar Jafar yasan tana sonshi akan su cigaba da zumunci matsayinsa na customers nasu.
Daga haka ta share batun ta ajiye wayarta ta hau aikin abincinsu na shan ruwa.....!
*********
Har akayi kwanaki biyar,azumi yana cikin kwana ashirin da d'aya. Bata k'ara kiransa ba,sai ana ashirin da biyu ta tsara text na barka da shan ruwa ta aika mishi a k'arshe ta sanya sunanta Hadiyya.
Shi kuwa lokacin yana faka mashin d'insa ne ya dawo gida. Jin shigowar message,yaja tsaki. Yana tunanin watakila ya chanja layinsa daga Mtn zuwa Airtel. Ya gaji da sakonni marasa kan gado da suke yawan turowa. Don haka bai ko bud'e ba ya share.
Ya tarar Bahijja tayi komai ta jera musu akan leda a k'asa. Bayan sunyi mishi sannu da zuwa ne ya shige d'akinsa. Saida ya soma kokarin sanya wayar a chaji ne ya lura message fa bana kamfani bane. Ya d'auka ganin lambar da yake tunanin ya tab'a saninta. Bayan ya kammala karantawa a k'arshe yaga sunanta. Abun ya tsaya a ranshi,toh ita kuma wannan yau d'inma kuskuren ne ko kuwa dai tana sane? Oho. Ya tab'e baki har zai goge sai yaga kyan yayi mata godiya. Don haka ya aika k'aramin sak'o gareta
"Jzk Allah khair. Sm 2 u."
Daga haka ya jona chaji ya tafi domin shan ruwa.
********
Ta nanata yafi sai talatin,sanyi ya mamayeta domin har ta fidda rai jin da tayi shiru baice komai ba. Mama ta tsura mata ido ganin tana ta doka murmushi
"Lafiya? Ko kema an maki kyautar dubu talatin d'inne a waya?"
Tayi dariya ta girgiza kai,ai wallahi Jafar ya fiye mata dubu talatin.
"Ko kusa,kawai labarin ban dariya kamfanin mtn suka aikomin ne."
Mama ta gyada kanta batace komai ba.
Tun daga ranar kullum Ladi saita turawa Jafar sak'on gaisuwa,har ta soma gundurarshi. Ita kuwa wannan 'yar godiyar da yake turo mata ne takejin dad'insa sosai. Saida taga har tayi sau uku bai turo ba yasa ta ja da baya gudun kada fa ya soma ganin bak'inta....!
*******
RANAR SALLAH...!