Rayuwar Jafar da Siyama sai godiyar Allah domin a kashi d'ari na k'azantarta,ta rage ashirin. Har lokacin dai shine mai yiwa kanshi gyaran d'aki da band'aki. Tun wata rana da tace ya bar mata zatayi. Dadi ya cikashi ya cire mukullayen daya had'asu dana mashin d'insa ya damk'a mata. Saidai fa ya dawo yaga ba daidai ba,domin saika ka rantse yarinya mai shekaru goma tayi gyaran,k'asan ma sai k'arni,da yayi magana tace ai daga mopper d'inne. Band'akin ma tashin k'arni yake,nan ma tace ita kam batasan matsalar ba. (Alhalin Dauda ne mai wankin toilet d'in).
Tun ranar ya daina bar mata mukullayensa acewarsa nauyi yayi nata yawa ga ciki ga ayyuka? Hakan yayi mata dad'i,har ma alokacin ta kasa b'oye farin cikin nata.
Watarana suna zaune a falonta,Siyama tana kwance tayi matashi da cinyarsa tana game d'in Candy Crush a wayarta. A hankali kuma yake shafa gashinta yana bin d'akin da kallo. Ya dubi sama yanda yaga Yana ta cika d'akin. Girgiza kansa yayi ya dubeta
"Siyama na tambayeki mana."
Ta dubeshi alamar tana saurare
"A gida bakya yiwa Hajiya aikin komai ne?"
Ta tab'e baki tana girgiza kanta
"Gaskiya Hajiya bata sanyani aiki,komai sai 'yar aikinta ce takeyi. Sannan kaima shaida ne batason bacin raina,koda an sanyani wani aikin girkin,musammanma yaya hanif yafi kowa matsamin anan bangaren. Matukar na b'ata raina Hajiya sai tace nayi zama na. Sukan yawaita yin fad'a da Hajiya akan ta hanani koyon aiki musamman girki wai wannan ba yi bane. Amma Hajiya saita bud'e mishi wuta. Akwai sadda Hajiya ta fita unguwa,Abba ya shigo ya hangi Saude a kicin tana fama da girkinsa. Ya k'araso d'akin Hajiya ya iskeni ina chatting. Wallahi Jafar saida ya zanemin jikina,sannan yace daga wannan ranar kada na k'ara tsallakewa har a gama aikin abinci bai ganni a kicin d'in ba.
Tun daga ranar na soma jagwalgwalawa har na iya kad'an kad'an,don sai naji muryar Abba nake fad'awa kicin d'in.
Kafin auren su anti rumaisa,sune masu yiwa Hajiya gyara sai bayan anyi musu ne Saude keyi. Hum,a wannan lokacin Hajiya shiyasa tafiso nayi aure da wani mai kudin wanda acewarta saidai ina kwance ayimin kowace hidima."
Jafar ya jinjina zancen bayan ta kammala,
"Ke kuma kika nace sai talaka ko?"
Ta muskuta tana duban fuskarta
"Kaima kasan alokacin ko yankani za'ayi,bazan fasa sonka ba."
Yayi murmushi kawai.
********
Misalin takwas na dare sukaci kwalliya ya dauketa a mashin sai gidan Haris. Dayake sun san da zuwansu,suna isowa Haris ya fito ya tarbesu da murna. Ya dubi Siyama
"Amarya munyi maki fushi."
Tayi dariya "Ayi hakuri,kaga mai laifi nan."
"Kuma fa gaskiyane. Ku k'araso mana."
Suka shiga,kamshi mai dad'i ya bugi hancinsu. Komai tsaf yake gwanin sha'awa. Yaron Haris mai suna Aliyu yana rarrafe abinsa. Jafar ya d'agashi cak yana mishi wasa sai b'angala dariya yakeyi. Yana son yaron,ji yake tamkar shine ya haifeshi. Haris yayi ciki yana kira
"Ummina! Ummina!!"
Jafar ya saci kallon Siyama wacce ke k'arewa gidan kallo cike da sha'awa. Ita kanta komai na falon ya burgeta,saidai ta soma tunanin Kawai don Ummin ta kasance 'yar gidan masu hannu da shuni shiyasa falonta ya k'awatu batasan cewa gyara ma wani abun bane!
Suka dawo tare da Ummi. Matashiya ce bata wuce shekarun Siyama ba,ashirin da biyar. Taci ado cikin doguwar rigar nan ta kanti 'yar yayi. Fuskarta ba wata kwalliya tayi ba daga hoda sai lipgloss data sanya amma tayi kyau. Tana murmushi ta zauna kusa da Siyama daidai lokacin da Jafar ke zolayarta
"Uwargidan Rahma."
Ummi ta harareshi tana dariya
"Wacece Rahma? Na gayamaku bana kishi da ita."
Haris da Jafar sukayi dariya,Jafar yace
"A'a fa maman Aliyu,kada fa kiga abu ya tashi gadan gadan ki nuna bakisan zance ba."
Ummi ta tab'e baki had'e da dariya
"Ai na gayamaka ko Albarka ne sunanta ni Ummi bata gabana. Yaje yayi aurensa mana. Nidai ka gayamasa kada ma ya had'ani da ita zaman gida d'aya."
"Ballantana ma ba auren nayi niyyar yi ba."
Haris yayi saurin fad'a cike da fargaba. Ya tuna farkon ranar da ta daga wayarsa yana band'aki jin mai kiran tace rahma ce, a daren basu kwashe da dad'i ba.
Ummi dai ta mik'e tana jan hannun Siyama
"Ku kuka sani, nidai na fadamaku sharad'ina amma ban hanaku aurenku ba. Kawata zo muje ciki ko?"
Jafar wanda ke dariyar mugunta ba tare da ya lura da hararar da Haris ke watso mishi ba yace
"Toh bari nayi mishi rakiya zance."
Bata ce uffan ba,haushin Jafar duk ya cikata. Ummi itama fa akwai kishi.
Suna shigewa,haris ya kai mishi duka
"Kaidai anyi d'an iska,wallahi yau fa ka had'amin bomb. Shikenan yau za ayimin bore."
Suka sanya dariya
"Ai gwara dai ka fad'a mata tun abu baizo ya kankama ba."
Haris ya girgiza kanshi cike da damuwa
"Nifa ina ganin na fasa auren nan tunda Ummina bataso na hakura. Ranar nan nake gayamaka kada kaso kaga da yanda muka shirya da ita."
Jafar ya girgiza kansa ya zama serious
"Ba don raya sunna kakeson yi ba dana baka shawarar ka hakura. Kai bari na fadamaka,kaga Siyama ta isheni a rayuwa. Banga wata a duniya da zata isheni kallo ba. Koda Allah Ya kaddaro zan k'ara aure ko?"
Ya tab'e baki yana girgiza kansa
"Badai don inaso ba,sai don KADDARA."
Haris yayi murmushi
"Nikam son Rahma nakeyi. Jafar ni kaina koda a mafarki ban taba zaton bayan Ummi zanso wata d'iya mace ba,duba dai ka gani. Ummi bata rage a komai ba,tana da tsafta ladabi da biyayya. Tana bani kulawa sosai da sosai,kawai dai a lokaci guda Allah Ya sanyamin kaunar Rahma a zuciyata."
Jafar ya jinjina kansa,shima fatansa Allah Yasa matarsa ta gyara d'abi'unta. Babu laifi dai a yanzu ana kokarin bashi hakkinsa,ana kulawa dashi,saidai har yanzu tsaftar ragaggiya ce ba kad'an ba.
Sukayita hira abinsu.
A d'aki ma Ummi albums na biki dana sunan Aliyu ta ajiyewa Siyama. Tana kallo suna hirarsu. Can Ummi ta fito ta jera abinci akan kafet bayan ta shimfida leda.
Suka had'u gaba daya,sai lokacin ummi ta sakarwa Jafar har suna dariya don d'azun ma kishi ne.
Basu bar gidan ba sai goma da mintoci na dare. Siyama ta samu alheri mai yawa a wajen Ummi dana sutura dana kaya! Tayi godiya sosai,suka rakosu har wajen mashin d'in Jafar sannan suka koma ciki.. !
**
Ladi tana daga cikin d'an d'akin da suke ajiye kayayyakin kwanukansu da tukwane harma da sauran tarkacensu na girki,kamar daga sama taji muryar Jafar suna gaisawa da Mama. Tayi wuf ta fito har tana kokarin fad'uwa. Suna had'a ido ta sauke ajiyar zuciya tana murmushin farin ciki. Kamar bashi ba,yayi y'ar k'iba.
Jafar yana dariya yace
"Yar nijar kwana biyu?"
Ladi fuska a sake ta gaidashi,taji dad'in ganinshi har ma ta kasa b'oyewa. Bayan sun gaisa tace
"Yayana ai kaine ka b'uya,shiru ba'a ganinka."
Jafar ya shafi sumar kansa
"Ya za'ayi,sai a hankali. Yau ai ganinan ko? Ya karatun?"
Ta d'ago ta dubeshi tana murmushi
"Karatu alhamdulillah gashi muna ta shirye shiryen zana jarrabawar karshe na sakandire. A sanyamu a addu'a."
Ya bud'e baki
"Ikon Allah,yanzu Ladi har zaki kammala sakandire? Kina kankanuwa dake?"
Taji babu dadi,ita fa bata daukar kanta a yarinya kwata kwata. Saidai gaskiyarsa,shekaru sha bakwai ai dole a kirata yarinya. Ta wayance da dariya cikin marairaicewa tace
"Yayana shekaruna sha bakwai fa."
"Oh kina nufin kicemin kin girma ko?"
Ya k'arashe yana dariya. Itama dariyar tayi ta mike
"Oh yayana,nikam bance ba. Za'a kawo wani abu ne?"
Yana murmushi yace
"Bani favourite d'ina saidai fa bada yawa ba."
Cike da farin ciki ta juya,Mamanta tana ta aikin zuba abinci a farantai ta sanar mata yanason tuwo. Kafin mama ta zuba ta mik'awa masu zaman jira nasu sannan ta koma ta karb'o mishi. Duk abunda takeyi idanuwanta bini bini suna gareshi. Hankalinsa yana kan wayarsa har ta dawo ta ajiye mishi. Yayi godiya. Ta koma ta zauna anan wajen Mama. Tana yi tana satar kallonshi daga ta lura zai kallo inda take sai tayi saurin maida kanta ga kwanukan dake gabanta. Can jimawa kuma ta k'ara kallonshi.
Mama tana lura da ita,murmushi kawai tayi cike da tausayin Hadiyya. Lallai kam ta fad'a son maso wani wanda k'arshensa bai fiye zama mai dad'i ba.
Sai bayan Jafar yayi musu sallama zai tafi ne,tayi saurin bin bayanshi. Mamanta ta bita da kallo tana mai mamakin me kuma ladi zata gayamasa? Fargabarta kada ya zamto zata ce sonshi takeyi,amma idan hakane bata kyautawa kanta ba.
Ita kuwa Ladi saida ta bari sun matsa kad'an daga shagon tace
"Yayana daman cewa zanyi ko zaka bamu lambarka,kaga daka jima baka lek'omu ba duk mun damu saidai sanin da mukayi kana da iyali bamu takura ba. Inda hali ko zaka bamu lambarka sai a dunga gaisawa wataran saboda irin haka ko?"
Jafar bai kawo komai ba,murmushi yayi yace
"Kuma nima nayi wannan tunanin,naso sanin gidanku sadda Mama tayi rashin lafiya. Allah baiyi ba."
Ya karb'i wayarta,'yar Nokia ce k'arama "express music" secondhand ce. Ya shigar da lambobinsa ya mik'a mata yana murmushi
"Gashinan 'yar nijar."
Tayi godiya,sukayi sallama yayi kasuwa.
Mama ta dubeta cike da zargi,Ladi ta sakar mata murmushi.
"Me kikace mishi?"
"Bakomai fa mama,lambarsa kawai na karb'a saboda irin haka idan ya tafi mukaji shiru kinga ai da dad'i muji ko lafiya, ko?"
Mama ta tab'e baki,suka cigaba da aikinsu.
*********
yanxu akapara..!