Anti Habiba salati takeyi tana k'arawa lokacin data gama sauraron maganganun da suke fitowa daga bakin Jafar.
"Wannan abu dame yayi kama? Amma kuwa Siyama ta bani kunya,inajin wai wai a bakunansu Husna(d'iyarta)kafin aurenku ashe gaskiyarsu suke fad'i? Eh lallai Siyama ta cika KAZAMAR GIDA."
Jafar ya dubi Antinsa da mamaki
"Oh anti,har su Husna sun sani amma babu wanda ya tab'a sanar dani?"
Ta harareshi
"Tayaya za'a sanar maka kakana? Ni kaina ban yarda ba da suka sameni da zancen. Koda ma an fad'amaka yanda ka zama majnunu Siyama ai ba yarda zakayi ba. Ko ka manta furucinka a baya na tuna maka? Cewa fa kayi Siyama ta mamaye dukkanin b'angarorin dake jikinka. Toh waye mai karambanin tarar ka da wannan zancen kakana?"
Ya tuntsire da dariya,daman yasan muddin ya kawo laifin Siyama wajen antinsa zaiji magana tunda har da ita cikin masu bashi shawarar ya hakura da ita alokacin da Hajiyar Siyama ta hura wutar kiyayyarta ga auren nasu. Amma ina! Son da yake yiwa Siyama bai bari yaji shawarar kowannensu ba. Ga kuma rabo daya riga ya rantse.
"Oh antina,nikam na kawo kaina. Nidai a taimakamin da mafita abar tuna baya."
Ta tab'e baki
"Zanje gidan naka,nafison na ganewa idona kafin musan abunyi idan ta kama sai mu maidata makaranta." Ta k'arashe da wasa.
Jafar ya k'ara sanya dariya,
"Haba anti,yarinyar da tayi hadda? A dai nemo wani hanyar."
"Shikenan zan zaunar da ita muyi magana,Allah Yasa a dace."
"Amin amin antina."
Ya jima a gidan anti habiba suna hirarsu da dariya domin antin tasa badai raha ba amma fa sam bata da kyau yayinda aka tab'ota. Tana da zafi ainun.
********
Misalin uku da rabi na ranar Talata. Siyama tana zaune a tsakar gidanta ta bararraje tana aikin karatun wani sabon littafi wanda takanas taje bakin asibiti ta siyo,tana yi tana taunar cingam abinta. Zanin atamfa ne a jikinta da bak'ar T-shirt,kanta ko dankwali babu.
Gefenta kayan wanke wanke ne tuli guda k'uda yana ta zarya akansu.
Daga d'aki kuwa,almajirinta Dauda ne ke faman shara bisa umarnin uwardakin tasa.
A haka Anti Habiba tayi sallama ta shigo gidan. Siyama ta mike da sauri,tabbas saida gabanta ya fad'i ganin anti habiba a daidai wannan lokacin da bata tab'a tsammani ba. Ta hau kame kame
"Wa alaikissalam,oyoyo anti. Ashe kina tafe amma Jafar bai sanar dani ba. Sannu da zuwa."
"Jafar?"
Anti Habiba ta nanata a ranta,suna ne mai girma a zuri'arsu tunda ya kasance sunan mahaifin Hajja. Ashe har a yanzu akwai matan dakan iya kiran sunan mijinsu gatsal basu ko jin nauyi a bakinsu?
Tana amsa gaisuwar Siyama tana k'arewa gidan kallo,ko iyakar wannan sun isa a kira Siyama KAZAMAR GIDA. Mamaki takeyi na yanda gidan mutum ke a haka har ma ta iya d'aukar littafi tayi zaman karatu.
"Anti ya kika tsaya? Ki shigo ciki."
Anti habiba ta jinjina kanta,ta cusa kanta a falon,daidai lokacin da Dauda ya kwashe shara ya fito daga k'uryar d'akin Siyama.
"Na kammala Hajiya,sauran ina?"
Siyama ta dubi anti habiba wacce ta zuba mata ido tana sauraron abunda zata ce. Ta dubi Dauda tana 'yar dariyar borin kunya
"Uhum,kayi wanke wanken tukunna."
Bayan fitar Dauda,anti habiba ta girgiza kanta ta soma magana cikin tsabagen takaici.
"Haba Siyama! Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Siyama kin bani kunya. Ashe haka kike? Kaiconki Siyama,menene amfanin iliminki? Gidanki kaca kaca ace har kina da damar daukar littafi kiyi zaman karatu? Kafin ma akai ga littafi,ki k'arewa jikinki kallo daga sama zuwa k'asa ai ko wata jahilar ta fiki kyawun duba. Uban me kike d'auka a karatun? Wane darasi ne aciki dake nuna ayi rashin tsafta? A baya koda kud'i aka cemin na yarda zaki aikata wannan shiriritar ni Habiba bazan amince ba! Inayi maki kallon 'yar kwalliya kuma 'yar kwalisa,menene dalilinki na chanja akalar rayuwarki yanzu? Ace almajirinki shine zai maki dukkan ayyukan gida? Ina laifin ma sharar tsakar gida da cefane,amma ina shi ina tsallake falonki har ya taka zuwa k'uryar d'akinki sirrinki?!"
Siyama duk ta tsure,tasan anti habiba bata dakyau wajen fad'a,ai kuwa sai yi takeyi babu kakkautawa. Tun Siyama tana durkushe har ta zauna ta soma sheshshekar kuka.
Karshe kuma ta shiga nasiha.
"Tsafta takan k'arawa mace daraja ta musamman a wajen mijinta. Babu namijin da a duniya zaiso rashin tsafta. Toh ni yanzu abunda yafi dauremin kai shine,tayaya kike ibada? Kina sane kuma kin karanta a makaranta komai na addini baya tafiya saida tsafta ko? Zaman aurenki ya sunansa?"
Anti habiba tana girgiza k'afa tayi kwafa
"Tab! Siyama kina da aiki."
Ta fad'a tana girgiza kanta,can ta k'ara dubanta fuska a yamutse
"Batun girki kuma fa Siyama? Kina kokarin yiwa mijinki?"
Siyama tana mutsistsika idanunta sai lokacin ta samu karfin gwuiwar tankawa
"Inayi anti amma Jafar bai damu da cin abincina ba."
Anti ta fusata
"Kika k'ara ambaton sunansa a gabana wallahi sai bakinki yayi jini yanzun nan! Ke ba abun kunya bane ki dunga kiran sunan mijinki babu sakayawa ba komai? Kai wallahi nayi tirr da halayenki. Ko a litattafan da kike karantawa banda kiji ana kiran honey,darling sweety ko kuma baban wance ko wane bakijin komai! Badai ki tsinci mace mai tarbiyyar arziki ba tana kiran sunan mijinta ba Siyama. Yanzu haka babu alamar jikinki yaga ruwa. Ji gashinki yanda yake tamkar dambun da babu mai. Gida babu gyara babu komai,a haka wane namiji ne zai so ya zauna har ya ci abincinki? Allah Yasa ma kin iya girkin ba jagwalgwalo kawai kikeyi ba."
Anti Habiba ta cigaba da yi mata nasiha mai ratsa jiki har tana tsoratata akan matukar bata gyara ba toh fa wataran a kwana a tashi Jafar aure zaiyi.
Bata bar gidan ba saida ta sanya Siyama a gaba ta gyara komai tana taimaka mata. Ta tsaya a gabanta har tayi girki anti tana fadan ai data dunga daukar litattafan soyayya gwara ta nemi na koyon girki. Ta sanyata tayi wanka,a wajen sutura ma abu ya gagara. Yawancinsu duk riguna ne zanin sun kod'e. Masu kyawun kuma babu wanki. A karshe dai dakyar aka samu riga da wando marasa nauyi ta sanya.
Bayan kammalawa anti ta dubi ko'ina, babu sauran gyara,sannan ta kalli Siyama.
"Toh yanzu ko kefa Siyama,kin koma tamkar wata sarauniya. Inda haka mijinki yake tarar dake tsaf tsaf me zai sanyashi fargabar dawowa gida akan lokaci?"
Siyama tayi murmushi tana sunne kanta k'asa,a karshe anti tayi mata sallama ta tafi bayan tayi mata alk'awarin aiko mata da spices da litattafan girke girke na boko dana hausa....!
Tun shigowarsa yake bin ko'ina na farfajiyar gidan da kallo. Ganin da yayi ko'ina fes sai k'amshi ke tashi ya fahimtar dashi antinsa tazo. Murmushi ya saki yana duban sararin samaniya yanda ake walkiya da iska mai ni'ima da sanyi. Fatansa Allah Yasa rayuwarsu ta d'aure a haka.
"Barka da zuwa."
"Unbelievable!"Jafar ya fada a ransa,ya d'ora da hamdala. Kallonta yakeyi tun daga sama har k'asa,tayi masa kyau sai k'amshi ke tashi daga jikinta.
Mamakinsa bai k'aru ba saida tasa hannu ta karb'i ledar hannunshi.
"Bismillah mana." Siyama ta fad'a,nauyi sosai takeji ta k'ara kiran sunan nashi hakanan tana jin kunyar kiransa da wani sunan da bata saba da bai saba jin ta kirashi dashi ba. Ta gwammace ta bar kiransa kwata kwata,gwara tayi zancenta kai tsaye.
Ya bi bayanta,har kofar d'akinsa. Ya mik'a mata mukullin da yake had'e dana mashin d'insa. Ta karb'a ba tare data dubeshi ba domin idanuwansa har lokacin sun gaza barin kallonta. Bayan sun shiga,Siyama ta taimaka mishi wajen rage suturar dake jikinsa. Jafar jinsa yake tamkar ba shi ba. Yana murmushi yace
"Nagode,ya babynmu?" (Kuji fa,yau Jafar harda tambayar baby?!)
Murmushin itama tayi alokacin da yake tab'a cikinta.
"Lafiyarsa kalau,bebin da ake mantashi?'
Dariya yayi yana mai juyawa ya fita, ganin ya nufi kicin tayi saurin dakatar dashi cikin sassanyar murya
"Ai na dafa maka ruwa na had'a,yana band'akina."
Duk da yasan bazai taddashi da kazanta ba yau,hakan bai hanashi jin fad'uwar gaba ba. Ya bita a baya har d'akin,band'akin a wanke a bushe tsaf. Yayi wankansa ya shirya,a'a, sai ya k'ara cin karo da lafiyayyen abinci an jera mishi. Ya zage yaci sosai,ita kanta ta lura yau mijin nata yafi koyaushe farin ciki.
Daren ranar sun farantawa juna,fatan Jafar bai wuce Allahu Yasa Siyama ta d'aure a haka ba. Baisan har yanzu akwai sonta mai yawa haka a ransa ba sai a wannan daren......!
"Nifa ba don komai na damu dashi ba,abunda kike zargi don Allah ki bari. Kwanansa goma sha shida fa rabon da ya ziyarci shagonmu koda da niyyar gaisuwa ce. Shiyasa na damu amma ba don komai ba."
Ladi ce ke wannan zancen,kanta akan cinyar Mahaifiyarta.
Mama tayi dariya
"Yanzu menene ya kawo dogon bayanin nan? Toh naji ba sonshi kikeyi ba,saidai kin damu dashi ko?"
"Eh,a matsayinsa na yayana."
Mama ta girgiza kanta tana mai tufkewa diyarta ta gashi
"Au haba,ashe yayanki ne? D'an babanki ne ko d'ana?"
Ladi ta mike zaune tana turo baki cike da shagwab'a
"Toh mutunci fa mukeyi,kema kinsha cewa yana da mutunci. Tayaya zaki had'a irina da namiji irinsa?"
Ta langab'ar da kai tana tab'e baki cikin sanyi tace
"Yafi k'arfina,ya kere ni Mama. Irinmu sai marasa gata."
Mama taji tausayin diyarta ya tsirga mata zuciya,ta kamo hannunta
"Waya fadamaki Sarah? Kina da Allah. Hakanan ni mahaifiyarki ina tare dake. Ba don ma mutuwa mai raba tsakani ba,da yanzu mahaifinki yana nan tare damu. Sannan ke ba macen k'i bace,bamu da kud'i bamu da kyau. Amma zuciyoyinmu masu kyau ne. Watarana zakiyi mamakin mijin da zai nemi aurenki Hadiyya. Kada ki dauki zancena a hagunce,ba lallai sai mai kud'i ba,kodayaushe addu'a na Allah Ya kawo maki mijin da zai jib'anci al'amuranki,zaibaki kulawa har karshen rayuwarsa."
Ladi ta sunkuyar da kanta tana murmushi
"Allah Yasa mamana."
"Amin Hadiyya. Don haka ba Jafar ba,sai kiga Allah Ya had'aki da wanda yafi Jafar. Ai shi Allah babu ruwansa da kud'i ko talauci,matukarYa kaddaro zaka auri mutum koda ace shine sarkin masu kud'in duniya,ko kuma shine wanda yafi kowa talauci."
Ladi ta jinjina kanta,tabbas gaskiya Mama ta fad'a. Ta damu da lamuran Jafar,hakanan tana tsoron ya kasance wannan yanayin da takeji a zuciyarta game dashi shine SO. Ambaton hakan saida gabanta ya fad'i.
Ta k'ara maida kanta cinyar mama idanuwanta a lumshe,murmushidauke akan fuskarta.
"JAFAR"
Ta maimaita sunan cikin ranta,a hankali ta soma ayyano kamanninsa. Dogo ne,baya daga layin kyawawa saidai bazaka kirashi mummuna ba. Yana da cikar suma,bashi da wani hanci saidai masha Allah akwai idanuwa.
Ta muskuta tana murmushi har a lokacin,duk shigar da Jafar zaiyi ita kam burgeta take. Bata fiye ganinsa da kananun kaya ba sai jefi jefi. Toh a ajiye duka wadannan ma a gefe,haka kawai take kaunarsa. Halayensa sukan burgeta matuk'a. Bashi da girman kai,baya daukar duniya da zafi. Yakan dauki kowane mutum da daraja,baya kyashin bawa kowa girmansa matukar ya girme masa. Wannan yasa shima mutane kan ga mutuncinsa sosai,ciki kuwa harda ita. Bata tab'a cin karo da namijin da ya burgeta ba irinsa. Kodayaushe bata sakarwa customers fuska,don batason abunda zai janyo wani cikinsu ya gayamata zancen banza kamar yanda wani ya tab'a gigin yi. Tun daga lokacin ta chanja fuska.
Jafar kuwa yawan zuwansa ne ya sanya ta saba dashi,saida ta lura shi d'in kamilin mutum ne sosai kuma yakan girmama mamanta. Abunda ya janyo mishi samun matsayi babba a zuciyar Ladi....!!!!
********
yanxu akasoma..!