TAMBAYA TA 1767
********************
Assalamu Alaikum malam gameda su gold din da muke siya su awarwaro, sarka, da yankunne, shine nake tambaya suma ana fitar musu zakkah? Idan ana fitar wa ya akeyi ?nagode.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Akwai sabanin Malami dangane da wannan mas'alar.
Amma sabanin nasu abinsa yadda suka fahimci hadisan maganar zakkar ne. Misali akwai hadisi daga Amru bn Shu'aib da babansa daga Kakansa (Allah shi yarda dashi) yace:
"Wata mata tazo wajen Manzon Allah (saww) tare da 'yarta. Alhali 'yarta din tana sanye da wasu Warwaro masu kauri na zinare. Sai Manzon Allah (saww) ya tambayeta "SHIN KINA FITAR DA ZAKKAR WADANNAN?".
Sai tace "A'a" Sai yace "SHIN ZAKI SO ALLAH YAYI MIKI AWARWARO NA WUTA DASU ARANAR ALQIYAMAH?"
Nan take sai ta ciresu ta Wurgar".
(Abu Dawud, Nisa'iy da Tirmidhiy ne suka ruwaitoshi).
Imam San'aniy yace :
"WANNAN HADISIN HUJJAH NE AKAN WAJIBCIN FITAR DA ZAKKAR KAYAN ADO. Kuma azahirin magana, babu wata maganar Nisabi anan. Tunda Annabi (saww) yayi umurni afitar ma wadannan kayan adon kuma gashi basu kai Uqiyah biyar din ba, amafi rinjayen zance.
Akwai maganganu guda hudu acikin wannan Mas'alar :
1. WAJIBCIN FITARWA : Shine fahimtar mazhabin Hadawiyyah da kuma Jama'a masu yawa daga magabata na kwarai.
2. BAI WAJABTA AFITAR BA : Bisa fahimtar Mazhabobin Imamu Malik da Ahmad da kuma wani Qaulin daga Shafi'iy (Allah ya rahamshesu). Sun dogara ne da abinda aka ruwaito daga wasu da yawa daga Magabata cewa basu fitarwa.
Sai dai tunda ga Hadisi ingantacce babu damar yin aiki da aathar (gurbin aikin magabata).
3. BAYAR DASU ARO, SHINE KAMAR AN FITAR DA ZAKKARSU - Kamar yadda Imam Dara-Qutniy ya ruwaito daga Sayyiduna Anas bn Malik da kuma Asma'u bnt Abibakrin (Allah shi yarda dasu).
4. SAU DAYA AKE FITAR MUSU DA ZAKKAH SHIKENAN BA ZA'A SAKE FITARWA BA : Haka aka ruwaito daga Sayyiduna Anas bn Malik awata ruwayar (rta).
Amma dai mafi bayyanar zance shine Wajibcin Fitarwar. saboda ingancin hadisin. Amma Malaman da suke ganin wajibcinta sunce Nisabinta shine Nisabin zinare da azurfa.
Amma kayan cin abinci na Zinare ko azurfa (kamar cokali ko Kofi ko kwano) wannan duk haramun ne agun musulmi yayi aiki dasu. Sai dai kuma duk da haka akwai zakkah akansu.
WALLAHU A'ALAM.