A ci gaba da binciken musabbabi da wadanda ke da alhakin kai harin ranar Jumma’a a birnin Paris, hukumomin bincike da ‘yan sanda sun bayar da sanarwa cafke daya daga cikin mutane Takwas din da suka kaddamar da munanan hare hare a Paris da suka yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 135.
Rahoton na su ya nuna cewa wani matashi Bafaranshe, mai kimamin shekaru 29 da haihuwa mai suna Umar Isma’il Mostefai yana daga cikin wadanda suka kai hare-haren. Sun kara da cewa sun gano maharin ne ta dan yatsarsa, a yayin da suke gudanar da bincike a wurin da maharan suka fi kashe mutane.
An dai ce Mostefai mutun ne dake da tarihin zama batagari, kuma mai son rungumar tsatssaurar akidar Musulunci. Hukumomin suna ci gaba da kokarin gano ko mutumin ya taba zuwa Syria.
Masu shigar da kara na gwamnati sun ce maharan, dauke da bindigogi samfurin ‘AK47’ da rigunan kunar bakin wake, sun raba kansu zuwa gida uku ne a yayin hare-haren, kuma ana fargabar ko wasun su sun samu tserewa.
A yayin da duk duniya na ci gaba da taya kasar Faranshi jimamin wadannan hare-haren, gwamnatin kasar ta Faransa tana bayyana cewa ba za ta daina bincike ba, har sai ta gano maharan baki dayansu.