Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya cire shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, Ibrahim Lamorde daga mukaminsa.
Kawo yanzu a hukumance ba a bayyana dalilan da suka sa aka cire shi ba, amma kuma wata majiya kusa da fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da sallamarshi daga aiki.
A karshen shekara ta 2011 ne, Ibrahim Lamorde ya maye gurbin Misis Farida Waziri a matsayin shugaban EFCC a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan.
Shugaba Buhari ya samu nasara a zaben shugaban kasar ne saboda alkawarin da ya dauka na cewar zai yi yaki da cin hanci da karbar rashawa a kasar.
Najeriya na da dimbin arzikin albarkatun kasa, amma cin hanci da rashawa sun sa ba a aiwatar da ayyukan ci gaban kasar dai-dai da kudaden haraji da kasar take samu.
Tuni dai aka nada Ibrahim Magu a masayi sabon shugaban Inec
sabon shugaban EFCC Ibrahim Magu
Tsohon Shugaban EFCC Ibrahim Lamorde
Title :
EFCC Tayi Sabon Shugaban Bayan Buhari Ya Cire Ibrahim Lamorde
Description : Sh ugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya cire shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, Ibrahim Lamorde daga mukaminsa. K...
Rating :
5