Rahotanni daga Nigeria sun ce Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci daukacin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya na da su yi murabus daga kan mukamansu.
Dazu dazun nan ne dai Shugaba Buharin ya kammala wata ganawa tare da manyan sakatarorin su goma sha bakwai a fadarsa da ke Abuja.
Wannan al'amari na zuwa ne a jajiberin rantsar da ministocin gwamnatin kasar.
Shugaban kasar bai bayyana dalilan sallamar manyan sakatarorin ba, amma dai a shekarun baya ana zarginsu na assasa cin hanci da karbar rashawar da ke faruwa a ma'aikatun gwamnatin kasar.
Za mu kawo muku karin bayani a nan gaba
Title :
Buhari ya sallami manyan sakatarori
Description : Rahotanni daga Nigeria sun ce Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci daukacin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya na da su yi murabus daga kan ...
Rating :
5