Tsohon shugaban kasan Najeriya na soja, Ibrahim Badamosi Babangida ya bayyana cewa baza ya kara neman wani mukami ba a Najeriya.
IBB ya bayyana haka ne a Mina, birnin jihar Nija a ranar Litini 10 ga watan Nuwamba, kamfanin dillacin labaran Najeriya ne ya ruwaito.
Babangida ya ki amsa wata gayyata da jam’iyyar PDP tayi mashi domin yazo a gyara jam’iyyar. Ya bayyana cewa shi yanzu ya zama dattijo kuma ba zaya kara shiga siyasa ba.
Yace “Zani shigaba da mutun ta akidar magabata wajen habbaka Najeriya, ba zani kara shiga siyasa ba. Shekaru 4 da suka wuce a Transcorp Hilton Hotel.”