Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce ba zai daukaka kara ba a kan dakatarwar da aka yi masa a wasansu da Stoke ranar Asabar.
Hukumar kwallon Ingila, FA ta zartar da hukuncin ne ga Mourinho mai shekaru 52, saboda a ladabtar da shi ga tsaurin ido da ya nuna wa alkalan wasa lokacin da Chelsea ta sha kashi da ci biyu da daya a hannun West Ham.
Mourinho ba shi da damar shiga filin wasan Britannia Stadium, amma zai taho da tawagar 'yan wasan sa, kuma yana da damar sauye- sauye lokacin wasan.
"Na hakura," In ji Mourinho. "Ba amfanin kalubalantar su domin ba za a yi nasara ba".
Daga bisani an tambaye shi ko yaya ya ji bayan an dakatar da shi ? Sai ya ce "Ai ka san abu ne mai wuya, saboda haka ka san ban ji dadi ba."