A Wani hoto daya sanya a shafin shi na sada zumunta yace: “Ina alfahari da goya ma Aisha Alhassan baya a lokacin zabe. Yanzu duk wata karamar yarinya dake so ta zama Gwamna ya samu abin kwaikwayo. Muna bukatar mata irin su.”
Idan za’a iya tunawa, kotu ta soke zaben Darius Ishiyaku na jam’iyyar PDP akan zaben 11 ga watan Afirilu da aka yi na jihar, inda ta bayyana Aisha Alhasssan a matsayin Gwamna.
Ishiyaku ya sha alwashin daukaka kara da shi da jam’iyyar shi. Sannan kuma ta zargi shugaban kasa da jam’iyyar APC da hada kai da fannin shari’a wajen murkushe jam’iyyar. Jam’iyyar APC ta maida martani inda ta bayyana ma PDP ta zargi kanta ba APC ba.
Title :
Atiku Ya Taya Aisha Alhassan Murna
Description : A Wani hoto daya sanya a shafin shi na sada zumunta yace: “Ina alfahari da goya ma Aisha Alhassan baya a lokacin zabe. Yanzu duk wata karama...
Rating :
5