An yi hasashen cewa kafin shekarar 2016 'yan gudun hijira a Nahiyar Turai zasu fi miliyan 3.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira na Tarayyar Turai ta fitar da rahoto inda ta ce 'yan gudun hijira a nahiyar sun fi dbu 282.
An gano cewa mutane 710 ne suka shiga nahiyar a farkon shekarar 2015 don ahaka ne aka yi hasashen cewa zasu kai miliyan 3 kafin karshen shekarar 2016.
Tarayyar ta ce tana yunkurin sassauta lamarin kafin karshen shekarar 2017.
Dangane da matsalolin ne shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel, Sigmar Gabriel shugban SPD da kuma Horts Seehofer shugabanCSU suka gana da juna don shawarwarin bada izinin zama kasar, bada gudunmuwa da kuma shirye shiryen hadewan 'yan gudun hijirar a kasahen ciki har da ma kirkiran wani katin daya da za a ba dukkanin masu nemana mafaka.
Sun ce da wadanna katuna masu neman mafaka zasu samu kulawa gurin kiwon lafiya da wasu taimako.
An kuma ce za a maida hankula a wasu kasashen Balkan a matsayin amşntaccen kasashe.