Rundunar sojin Najeriya ta ce daya daga cikin 'yan kungiyar Boko Haram din nan guda 100 da ta tallanta nemansu ruwa a jallo, ya zo hannu.
A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Najeriyar, Kanar Sani Usman Kuka-sheka, ya fitar rundunar ta ce a jiya ne Hukumar zirga zirgar jiragen saman Najeriya ta kama wani mutum mai suna Chindo Bello wanda kuma ake kyautata zaton dan kungiyar Boko Haram.
An kama wanda ake zargin ne dai a lokacin da yake kokarin hawa jirgin Aero Contractors daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja zuwa Lagos.
Tuni kuma hukumar ta damka wa rundunar sojin kasar wanda ake zargin domin bincike.
A 'yan makonnin da suka gabata ne dai rundunar sojin ta Najeriya ta ayyana neman mutane 100 ruwa a jallo wadanda take zargi da hannu wajen kai hare-hare a wurare daban daban a fadin kasar.