Wata Kungiya mai rajin kare hakkin bil Adama ta ba sabon ministan tsaro kwanaki 7 akan ya fiddo da takardun shaidar karatun Shugaba Muhammadu Buhari.
Kungiyar mai suna Centre for Human Rights and Social Justice ta bukaci Dan Ali da kuma shuwagabannin soja dasu fiddo da takardun.
Jaridar Daily Post ta bayyana cewa sun bada kwanaki 7 ne domin a fiddo wadannan takardun. Kungiyar ta bayyana cewa ya kamata Shugaba Buhari ya basu umurni da su fiddo da takardun shi wanda yayi amfani dasu ya shiga aikin soja.
A lokacin yakin neman zabe, Shugaba Buhari ya bayyana cewa takardun nashi suna hannun hukumar soja. Kungiyar ta bayyana cewa idan dai bai fiddo dasu ba to wannan Na nuna cewa: “Yayi karya mafi muni duk da ana cewa shi mutumin kirki ne.”
Shugaban kungiyar Kwamared Adeniyi Alimi Suleiman ne ya bada wannan takardar manema labaran. Ya kuma bayyana cewa baza suyi wata wata ba wajen rubuta ma kasashen duniya idan dai har cikin kwanki 7 basu fiddo da takardun ba.
Title :
An Bukaci A Fito Da Takardun Buhari
Description : Wata Kungiya mai rajin kare hakkin bil Adama ta ba sabon ministan tsaro kwanaki 7 akan ya fiddo da takardun shaidar karatun Shugaba Muhammad...
Rating :
5