Alamomin cikawa da imani guda 21 – sheikh Aminu Daurawa
Wannan duniyar cike take da rikici, da musifu, da bala’o’i, da tashin hankali da jarrabawa, da matsaloli, babbar nasara shine, cikawa da imani,
Malamai sunyi bayanai gamai da wasu alamomi, idan mutum ya cika da su, ana yi masa fata na gari Sune
1- cikawa da kalmar shahada
2- mutuwa da gumin goshi
3- mutuwa a daren Juma’a ko ranar Juma’a
4- Shahada a filin yakin daukaka Addinin Allah
5- Mutuwa a tafarkin Allah
6- mutuwa da Annoba
7- mutuwa da sababin ciwon ciki
8- mutuwa da dalilin nutsewa a ruwa
9- mutuwa karkashin gini
10- mutuwa da kunar wuta
11- mutuwa da ciwon kaluluwa
12- mace ta mutu a wajen haihuwa
13- wanda aka kashe shi, wajen tsare dukiyar sa
14- wanda aka kashe shi wajen tsare iyalan sa
15-wanda aka kashe shi, saboda addinin sa
16- wanda ak kashe shi wajen kare kansa
17- wanda ya mutu da ciwon tarin fuka
18- wanda aka kashe shi, akan hakkin sa
19- wanda ya mutu wajen gadin addini da dukkiyar
Al’umma
20- wanda ya mutu yana cikin aikin alkhairi, kamar sallah dawafi, azumi sujjada, da makamantansu,
21- wanda ya mutu mutane suna ta yi masa sheda ta gari, Dalilan wadannan bayanai, daga littafin Allah da sunnar Annabi saw, suna cikin littafin Ahkamul Janaiz na Shaik Albaniy da salatul Mumina na Dr Saeed alqahdaniy, Allah yasa mu cika da imani.