Tsaye yake kofar dakin kula tare da yin aikin gaggawa na asibitin yana kaiwa da komowa, mintuna talatin kenan da kawowa kuma likitoci suka hau aiki amma ba wani bayani har izuwa yanzu.
Zuciyarsa nata yi masa sake-sake kala-kala, me yasa zaiyi haka?? Don me ma ya ma zan takura akan abun da bai shafeni ba?? Kada fa nayi silar kashe yar mutane ko na jawo mata w...........
Hango fitowar likitan daga dakin da yayi ne yasa ya dakata daga zancen zucin da yake yi ya tunkari inda yake da gaggawa, doctor ya akai?? ya ake ciki?? zata lafiya kuwa??
Ya tambaya cikin tashin hankali.
Likitan ya dubi nurses din dake tare dashi yace " kuyi ku samo abin nan yanzu ".
To suka fada tare da wucewa.
Ya juyo ga ahmad yace " Karka shiga damuwa da yawa zata sami sauki bada jimawa ba insha Allah, mun shawo kan abin sai dai har yanzu bata farfado ba.
Idan mahaifinta ko mahaifiyarta sunzo ina son ganinsu a ofis."
Ya wuce da sauri.
Ahmad baiyi wata-wata ba ya fada dakin kai tsaye izuwa gabanta yabi ta kallo cikin sanyin jiki, ALLAH SARKI humaira zuciyarsa ta fada.
Ya danja da baya ya zauna a kujerar dake gefen gadon da take kwance har yanzu idonsa akanta yake.
Abinda ya fara fado masa arai shine: Tayaya za'ai iyayenta ko wani nata yasan halin da take ciki tunda bashi da zabi dole sai hakan ta faru.
Tuno da wayarta da yayi wacce ke rike a hannunsa yasa yayi saurin dagota kai tsaye ya shiga contacts dinta, abin mamaki ba wasu lambobi ne da yawa a ciki ba, ya tsa ya a dai dai lambar da aka sa MY MUM, ya danyi jim kamar me jin tsoron kiran bisa dole ya danna kira tare da karata a kunnensa.
Yayi shiru ya kasa magana har sai sanda wacce ta daga wayar tace " humaira lfy shiru har yanzu??
Ahmad dakyar yace " ba ita bace ni sunana Ahmad ina fatan kece mahaifiyarta??"
Ehh... nice.... mahaifiyarta lfy dai ko??
Ta tambaya da sauri.
Humaira ta yanke jiki ta fadi yanzu haka muna asibiti...."
Subhanallahi!!!! Ta fada cikin rudewa tare da cewa kuna wane asibitin ne??
Ahmad cikin sanyin murya yace " ALBARKA HOSPITAL dake nan cikin........."kafin yakai karshen maganar ta katse wayar.
Yabi wayar da kallo lokaci guda ya juya ga fuskar humaira yabi ledar ruwan da aka jona mata da kallo izuwa inda yake a rataye can sama, ya dafe kai, ko kadan baya son kallonta musamman idan ya tuno abinda ya faru kafin shigarta halin da take ciki.
mintuna talatin ya sake shafewa kafin mahaifiyarta da wata da baisan ko wacece ba suka zo, da tambayarshi suka fara.
Ahmad yace " muna cikin magana to sai ta mike lokaci guda kuma ta yanke jiki ta fadi.
mahaifiyartata tace " to yanzu me likitan yace??"
Ahmad yace " cewa yayi idan wani yazo daga cikinku yana bukatar ganinsa.
Mahaifiyar tata ta dafe kai tace " humaira ban taba ganin mutum irinki ba, ace ke ba zaki taba manta baya ba? ba zaki taba daina tunanin abinda ya wuce ba? Wasu hawaye suka gangaro mata, wacce suka zo taren ta fara rarrashinta, Ahmad kuwa binsu kawai yake da kallo.
Ta juyo ga Ahmad tace " sai kayi kokari ka tafi tunda munzo kada dare yayi maka.
Ya gyada kai kawai ba tare daya motsa ba, ya dade kafin ya tashi ya mika musu wayar humairan kamar mara laka a jiki a haka ya fita daga dakin.
zuwansa motarsa keda wuya yayi arba da jakar humaira ya dago ta tare da jujjuyata a hannunsa yasan tabbas tana ji da kyakyawar jakar tata sbd kusan kowanne lokaci da ita yake ganinta.
Kamar ya fita yakai musu ita sai kuma ya fasa ya jawo kofar motar tasa ya kunnata yabar harabar asibitin.
Jikinsa a sanyaye yake tukin, jinsa yake kamar sabon mara lfy a haka ya iso gida, da sauri ya wuce izuwa ciki yadda yake so kuwa momi bata falon sai saudat kadai kwance tana danna wayarta.
Ta amsa sallamar tasa kanta nakan wayar tare da cewa yaya ka dawo??
Ehh... na dawo ya fada tare da wucewa da sauri kafin ta dago kai izuwa dakinsa, dai dai sanda ta tashi zaune tabishi da kallo a ranta tace " Wannan lfy?"
jim kadan ta dan daga kafada tare da komawa ta kwanta.
Yana shiga dakin nasa ya mayar da kofar ya rufe ya jingina a jikinta idonsa ya ciko da kwallah a hankali ya karasa ya jefa jakar tata kan makeken gadon dake dakin, fadawar jakar keda wuya ta bude abinda ke cikinta ya fito wanda yayi saurin canja fuskar Ahmad.
Wani katon littafi ne me tsawo, fadi da yawan gaske.
Ya zauna a gefen gadon a hankali ya jawo littafin ya kare mai kallo a haka a hankali kuma ya bude bangon littafin idonsa yayi saurin kara zarowa sanda yaci karo da hoton humaira me matukar kyau da haiba a kasa an rubuta AISHA HUMAIRA ISMA'IL ya karewa hoton kallo sannan ya bude shafin gaba anan ma hoto ne amma ba nata ba, wani kyakyawan saurayi ne da shekarunsa basu haura Talatin da daya 31 ba, kyakyawa ne na gaske a kasan sunan nasa ansa UMAR FARUK ABUBAKAR, Ahmad ya dade yana kallon hoton nasa ya sake bude shafin gaba nan kuma hotuna ne nata da wancan faruk din a samansu ansa FARUK & HUMAIRA, tsakiyarsu kuma dan gaf fin dake tsakaninsu ansa ONE LOVE!! daga kasa kuma ansa LIFE TOGETHER DIE TOGETHER.
Littafin ya subuce daga hannun Ahmad sbd mamaki, dama halin da take ciki akan soyayya ne??
Waye kuma wannan faruk din??
Tambayoyin da suka fara zuwar masa kenan.
Ya sake cakumo littafin da sauri ya bude shafin gaba na tafkeken littafin yaci karo da abinda yasa shi saurin gyara zama CIKAKKEN LABARINA.
labarin humaira kenan?? ya tambayi kansa, yayi saurin gyara zamansa ya karasa karanta abinda aka rubuta a kasa, labarin farin ciki na gajeren lokaci daya jawo bakin ciki na har abada.
Labari me tsuma zuciya da sanya shauki.
Labari me tare da tarin Al'ajabi.
Ahmad bude shafin gaba ya fara karanta labarin humaira daya dade yana burin ya sani.
Cikakken SUNANA Aisha humaira, sunan mahaifina Alhaji Isma'il ishak daya daga cikin hamshakai kuma fitattun yan kasuwa a africa.
Haifaffiyar garin kano unguwar hausawa......kuma SABAHUL KHAIRI...
Shine yadace da masu karatu..
Se ku qara gyara xama dan sauraro da karanta labari me cike da AL-AJABI....