hakan na iya faruwane kawai idan fyade akayi mata, kaga ta tashi daga budurwa, kuma ba bazawara bace sannan ba matar aure ba.
Ahmad yayi shiru cikin salo na nazari jim kadan ya girgiza kai yace ' gaskiya baki fada dai-dai ba wacce aka yiwa fyade ai ta zama bazawarako??"
Saudat tayi shiru kawai tabishi da kallo, tabbas yafi ta gsky kuma ba dai-dai ta fada ba.
Ahmad yadan harareta kadan ya tashi izuwa kujerarsa yace " ke dama idan ba danna waya ba me kika sani??"
Saudat tace " to ai ko ba komai nayi kokari 2nda nayi tunanin abinda kai baka yiba."
Ahmad ya kauda kai yace " kinyi tunani amma useless ne ".
Tabishi da kallo tace " kasan abinda za'ai? ".
Ya girgiza kai alamar A'a.
Tace "bari mu tambayi momi 2nda ita tsohon hannu ce ta yiwu ta sani sai ta fada mana," Ta yunkura da nufin kiran sunan MOMI, Ahmad yayi saurin dakatar da ita yace " KE! rufa min asiri, bari don Allah. "
Ta kwantar da kanta jikin kujerar ta kyalkyale da dariya tace " Amma dai yaya duk sanda ka samo wannan amsar don Allah nima ina jira sbd ina son nasan yadda akai hakan zata faru don nidai ina ganin da kamar wuya....."
Ahmad ya mike rike da jakarsa yace " kada kiyi saurin karyata abinda baki sani ba, kiran salla ake bari na shiga ciki nayo alwala. "
Tabishi da kallo kawai har ya shige dakin nasa, ta juya ta kwanta bisa doguwar kujerar tare da cigaba da danna wayarta.
*********** **************
*** BAYAN SATI GUDA ***
Zaune take cikin faffadan ofis din ita kadai ba tare da kowa ba, babu alamun motsin wani tsit ofis din yake sai dai na'urar dake nuni da shigowar sako dake kadawa a hankali lokaci zuwa lokaci.
laptop ce a bisa tebirin dake gabanta gefe guda takardune da files tuli da ita kanta bata san adadin suba.
Sai dai gaba daya hankalinta da 2naninta ba akan aikin dake gabanta yake ba, uban tagumi kawai ta zuba da dukkanin hannayenta biyu, glass din data saba sakawa a idonta ajiye yake a gefe wanda hakan ya fito da hawayen dake zubawa a idanunta a zahiri.
100% na hankalinta ya tafi ne ga karanta wasikar jaki, koda ba'a fada ba tabbas abinda take tunani nada alaka da wani matsanancin yanayi da take ciki.
uk da na'urar dake huro iska tako ina daga sassan ofis din amma hakan bai hana ta hada wani zazzafan gumi ba wanda ke ketowa daga sassan jikinta, hadewar da gumin fuskarta da hawayen dake kwaranya daga idonta suka yine yasa suka jika takardun dake gabanta sharkaf.
Nisan da tayi yasa bata ji shigowarsa ba duk da sallamar da yayi ta kwalawa, Ahmad yayi turus a gabanta yana dubanta kawai dai dai sanda fuskarsa ta canja daga murmushin da yakeyi, ya zauna a kujerar dake fuskantarta sai dai har yanxu bata dawo hayyacinta ba bare ta fahimci cewa wani ya shigo inda take, da alama bata ma san a inda take ba.
bayan ya gama yi mata kallon AL'AJABIN ne kuma ya kira sunanta.
HUMAIRA hade da dukan tebirin dake gabanta.
Firgigit! tayi tamkar wacce ta tashi daga barci, tabi inda take da kallo kamar wacce ta ganta a sbn waje.
Lokaci guda tayi kokarin goge hawayen dake idonta ta kakalo yake ta maye gurbinsa dashi tace " Ah....Ahmad yaushe ka shigo??"
Ya dan bita da kallo yace " Humaira kukan me kikeyi??"
Tayi saurin girgiza kai tace " kuka kuma? ni... ba kuka nake yi....ba."
Ahmad ya danyi guntun murmushi yace " Humaira a rayuwa damuwa bata taba buya domin ita abace da ba a zuciya kawai take zama ba rubutu takeyi da manyan baki akan fuska wanda kowa sai ya gani, kuma koda ma tana buya to ta yiwu girman taki damuwar ta wuce a boyeta don da zata boyu da kin boyeta.
Ya rankwafo da kansa gareta yace " Me zai hana ki bani dama nasan wani abu a rayuwarki, ta yiwu ina da hanyar taimakonki koda da addu'a ne."
Idan kana yiwa Allah ka daina yimin wannan maganar ba wani dalili da zaka damu sai kasan labarin rayuwata, Aikine kawai ya hadamu dakai ka tsaya a iya haka ko don tsare mu2ncinka a idona."
Ahmad ya daga kafadarsa kadan yace " 2nda ba zaki fada min ba shikenan, dama nazo ne na sanar dake gobe muhimman kayan aikinki zasu karaso saiki shirya."
ya mike tare da cewa " see U next time ".
Ahmad!! Ta kira sunansa dai dai sanda yake gaf da ficewa, ya tsaya cak a hankali kuma ya dawo izuwa gabanta.
Ta dago kai tace " Don Allah kayi hakuri kayi min uzuri kwakwalwata ce ba zata juri tuno dukkan abinda ya faru dani a baya ba, amma ta yiwu wata rana ka sani."
Ahmad ya zauna bisa kujera yace " Humaira wasu lokutan kunshe abu a rai cuta ne furtashi kuma warakane, yana da kyau na rike wani hujja koda guda dayane wadda zan rika nayi miki uzuri idan na ganki a yanayin dana ganki yau.,"
Hawaye suka sake gangaro mata idanunta suka bude karrr tace " Tunda uwata ta haifeni ban taba ganin mutum mara yarda ba irinka, baka taba yiwa mutum uzuri? kai kawai abinda kake so shine a ranka??
To bazan fada maka ba, tunda baya cikin sharadin abinda dole sai ka sani kafin ka zauna dashi, idan ka kara yimin wannan tambayar ba zaka kara ganina ba har abada. Akan me?? Ta fada da karfi sannan ta dora " Na zabi nayi aiki ne badon kudi ko don na samu wani abu ba sbd nafi karfin wannan, sai don ina tunanin hakan zai rage wani yanki na damuwa idan kuma kace takurata zakai kake bijiro min da wata damuwar abu me sauki na hakura."
Takai karshen doguwar maganar tata da ajiyar zuciya.
Ahmad yace " Nida kike ganina mutum ne me son samun labarai musamnan na al'ajabi, daga cikin labaran dana samu akwai a 2nanina naki shine zai zamo na farko a ban al'ajabi, baki da wani zabi dolene nasan labarinki a yau."
yakai karshen maganar cikin daga murya.
Lokaci ta kara sauyawa ta hade rai ta kara fusata gami da harzuka ta kauda kanta domin ta gama zuwa iya wuya, Dame wannan mutumin yake takama daya isa yayi mata dole.
Ta mike ta rufe laptop din dake gabanta ta jefa masa mukullin ofis din ta jawo babbar jakarta ta rataya cikin tsawa tace masa " Don ina aiki dakai ba yana nufin ka cutar da kwakwalwata bane, idan badon na kaskantar da kaina ba kai nafi karfin kayi min dole wlh.
Ga mukullinku nan tafiyata itace mafi sauki daga wannan matsin lambar taka.
Ta ture kujerar kusa da ita cikin sauri ta nufi kofar ficewa.
Ahmad ya jawo mukullin ya rikeshi a hannunsa cikin sauri ya waiga kafin ta fice yace " Ba wani abu bane idan kin tafi hakan shine ma ya tabbatar min da mummunan zargin da nakeyi akanki."
Duk da batai niyya ba amma sai da tayi saurin waigowa duk da cewa daf take da ficewa.
Ahmad ya juyo sosai ya dora da cewa " Na yarda da cewa ke MUGUWA CE, tabbas ke ba mutuniyar kirki bace, a rayuwarki babu komai sai ta'asa da rashin kirki, na tabbata wani mummunan abu kika aikata wanda yake bibiyarki kuma ya hana miki kwanciyar hankali......"
Ya dakata da maganar yana kallonta.
Idanunta suka zaro kamar zasu fado 'iiihhhhhhh!!!!' bakinta ya fada dai dai sanda ta rike bakin nata, zuciyarta ta fara saka mafi munin maganganun da aka fada mata, lokaci guda kwakwalwata ta gaza jurar amsar kalaman, kanta yayi nauyi tayi saurin dafeshi, idanunta suka fara juyewa wanda yazo dai dai da sanda kafafuwanta suka gaza daukar gangar jikinta, cikin sauri kwakwalwarta ta tuno mata abinda yace.......
Na yarda da cewa ke muguwa ce, tabbas ke ba mutuniyar kirki bace, .......... na tabbata wani mummunan abu kika aikata daya hana miki kwanciyar hankali......
Dai-dai lokacinne ta karasa sulalewa kasa cikin yanayi na suma....
Wai wai wai wannan al'amari akwai rikici..
Kubiyoni anext..