Ahmad yaci gaba da kallonta kawai har yanzu mamaki ne cike fal kuma rubuce a fuskarsa, Abinda ke yawo a zuciyarsa shine:
Babu alamar wasa a tare da ita, hasalima hawayene ke zuba bisa idanunta a halin yanzu kuma gashi ta rantse, Tabbas hakan na nuni da cewa har cikin zuciyartane abinda take fada.
abin AL'AJABI mafi girma da kunnuwansa suka taba jiye masa kenan.
Tunani daya da yayi wanda ya kore 2nanin da yakeyi a baya shine: To kodai don ni namiji ne yasa ban fahimci abinda take nufi ba??
Tabbas shine dalilin.
Ya bawa kansa amsa dai-dai sanda ya dubeta tare da zaro wasu takardu dake gabansa ya dora a gabanta yace " Yanzu dai shikenan kiyi hakuri ki daina kuka ga kundin takardun da kike bukata a aikinki bari nasa masinja yayi miki jagoranci izuwa ofis dinnaki, daga yau kece babbar me kula, da adana bayanai na wannan ma'aikatar ALLAH YA TAYA RIKO."
Yakai karshen maganar dai-dai sanda ya waiga tare da kiran sunan masinja, BALA!! BALA!!!
Da sauri ya karaso tare da dukawa yace "Yallabai".
Ahmad ya dan kwantar da kansa bisa kujerar da yake zaune yace " Kuje da ita ofis no: 11 ka hadata da sakatariya zanyi mata waya."
Da sauri bala masinja ya amsa da " To Yallabai " Ya wuce yayi gaba.
Humaira dake zaune ta mike ta jawo jakarta wadda ta dade da dorata bisa faffadan tebirin dake gabanta, ta debi takardun da Ahmad ya bata ta zuba a ciki tare da gyara zaman bakin glass din dake da fadin rufe idonta daya matukar kara mata kwarjini.
Ta dan bishi da kallo kawai ta juya ta nufi kofar fita daga ofis din, Yayi saurin cewa " Koda ba yanzu ba ina fatan na sami labarin rayuwarki wanda ta yiwu ya warware min rudanin dana ke ciki."
Tayi saurin dakatawa tare da dawowa da baya a hankali tace " Idan har ba kana yin haka bane don ka gano hanyar karya zuciyata ba to na rokeka ka bari, ka kalleni a humaira kawai karka takura wajen binciken wacece ni sbd ba abune me samuwa a wurinka ba, Ta dan kara daga muryarta tace " Bakina bazai taba iya furta labarin daya faru dani a baya ba kamar yadda kwakwalwata ba zata juri tunano hakan ba, idan kana son mu zauna lfy dakai karka kara taso min da wannan zancen."
Takai karshen zancen cikin tsawa a dai-dai lokacin data canja gaba daya kamar ba ita ba.
Taja da baya ta fice da sauri.
Ahmad ya bita da kallo lkc guda ya mike izuwa tagar ofis din ya hangeta ta glass kai tsaye wata tsaleliyar mota kirar TOYOTA PRADO ta dosa ta bude motar ta shige, motar tata tabi bayan tsohuwar HONDA CIVIC wadda bala masinja keja don yi mata rakiya.
Ahmad ya kauda kansa daga wurin ya fara takawa a hankali cikin ofis din, Yarinyar nan fa ba karya takai tayi takama ko gadara, kallo daya yayiwa motarta yasan ta fito ne daga gidan masu akwai, to amma meye mummunan abinda ya faru da rayuwarta har yasata shiga yanayin da take ciki?? menene musabbabin hakan??.
Abin nema ya samu don haka wlh sai na sani kota halin kaka.
Ya fada a fili, ya juya ya rufe laptop dinsa tare da jawo bakar jakarsa ya zirata a ciki, jakar tasa na hannunsa yayi waje.
Kai tsaye motarsa ya nufa yabi tsaleliyar hanyar data nufi kudu, a ransa ya darsa cewa ya fasa zuwa inda yayi niya 2nda yamma ta riga tayi.
Duk da sanyayyar wakar mawaki justin bieber dake tashi a hankali cikin motar tasa baisa ya manta da abinda ke ransa ba.
Mintuna Ashirin ya kwashe ya gangaro cikin katafariyar unguwar tasu, rukunin gidaje na NEWCLAX QTRS. tsararriyar unguwa ta gani da fada.
Worn daya yayi a bakin tafkeken koren gate din ya fara budewa a hankali bisa jagorancin wani siririn matashi wanda yayi saurin cewa " sannu da dawowa ".
Ahmad ya gyada kai tare da fadin yauwa.
Ya wuce da motar yayi parking dinta a harabar gidan ya wuce izuwa cikin, shigowarsa falon keda wuya yaji kyas!! Alamun daukar hoto, yar kyakykyawar budurwar ta tuntsire da dariya tace " gaskiya yaya hoton nan yayi kyau, bari a kara maka daya."
Ya dan harareta kadan yace " ke baki da wani aiki saina daukar hotunan mutane a waya ko??"
Ya karasa ga daya daga cikin kujerun dake zagaye a katafaren falon, momi dake zaune kanta na kallon TV din dake jikin bango ta juyo gareshi tace " Ahmad an dawo kenan??"
Wallahi momi sai yanzu,
Ya fada cikin ladabi.
Dai-dai lokacinne saudat ta dire farantin juice dake hannunta ta tsiyayo lemon a dan karamin kofi ta mika masa, Ya amsa tare da cewa " Thank U my blood sister, yau dai kina da kirki ".
Ta juyo tace "yau kawai??"
Ya gyada kai yace " iya yaune kawai ".
Ta juya ga momi dai dai sanda ta karasa ga kujera ta zauna tace " momi kinji shi ko??".
Momi ta mike tare da cewa "zaku fara surutun naku kenan? to bada ni ba bari na shiga ciki lokacin sallah ya gabato."
Shigewarta sashin nata keda wuya Ahmad ya dawo kujerar da saudat ke zaune yace " yauwa ina da tambaya watakila keki sani don nidai nayi iya tunanina na kasa ganowa amma fa gsky zaki gaya min pls".
Tayi murmushi tace " fadi muji idan na sani ".
Ya gyara zama yace " Tayaya mace zata zama ba budurwa ba, ba bazawara ba, kuma ba matar aure ba?? Sannan da wane suna za'a kirata?? "
Saudat ta danyi shiru can tace " waye yayi maka wannan tambayar?"
Ya girgiza kai tare da cewa " ba ruwanki kawai ki amsa min idan kin sani ".
Saudat ta kyalkyale da dariya tace " Amma yaya anyi saurin juya 2naninka daka kasa gano amsa me sauki irin wannan, mace na iya zama ba bazawara ba, ba budurwa ba, ba matar aure ba IDAN..........!?¿¿