Tsaye yake ya dafa tebirin dake gabansa tare da rankwafawa kansa na kallon tebirin dake gabansa, kallo daya zaka yi masa kasan a cikin damuwa yake.
Ya dago kansa tare da matsawa yaci gaba da takawa ya fara safa da marwa a cikin faffadan ofis din nasa, tsawon lokuta ya shafe yana kaiwa da komowa ya rasa me ke masa dadi.
A tsayen ya zura hannunsa ya zaro wayarsa dake al‘jihu ya lalubi lambar wanda yake son kira tare da karata a kunnensa ya taka a hankali izuwa kan kujerarsa ya zauna, hannunsa daya na rike da wayar yayinda dayan hannunsa ke dafe bisa tebirin dake gabansa.
Hello!! ya fada dai-dai sanda aka daga wayar sannan ya dora da cewa “ Ranka ya dade yarinyar nan fa har yanzu bata zo ba ina tsammanin ma ba zuwa zata yi ba, gaskiya na gaji ga yamma na dada yi kuma na gaya maka uzuri gareni ga yamma na dada yi.“
Cikin rarrashi wanda ake yiwa wayar yace “ Ahmad kayi hakuri ta taho go slow ne ya riketa amma yanzu zata karaso.“
Ahmad din ya kara bata rai ya kauda wayar daga kunnensa ya ajiye wayar bisa tebirin dake gabansa ya kwantar da kansa jikin kujerar ya zubawa kofar shigowa ofis din ido, sai daya shafe wasu mintuna ashirin din babu alamun wani zaizo sbd takaici runtse idonsa yayi kamar barci yakeyi sai dai a zuciyarsa 2nanin irin fadan dazai rufeta dashi kawai yake.
As-salamu-alaykum.
Wata zazzakar murya tayi sallamar data saka Ahmad saurin dago kai tare da gyara zamansa yana me kallonta har izuwa sanda ta zauna tana me fadin “gani na iso“.
2nanin da yake tayi a baya sai yayi saurin kawar dashi domin kallo daya yayi mata yasan tafi karfin wulakanci ko a tozartata ba karamin kwarjini gareta ba, zunzuru2n kyau kuwa ba‘a magana lallai Allah yayi halitta.
ya fada a zuciyarsa.
Amma dai kinsan kin bata min lokaci ko??
ya fada yana dubanta.
ba tare da alamun nadama ba tace “ Eh nasani “.
To me yasa?? koda dai ance wai go slow ne ya rikeki??
Ya tambaya ba tare daya dubeta ba shima.
Tayi saurin girgiza kai tace “ gaskiya karyane hasalima ban taba hawa titi fayau irin yau ba, ni din ce kawai ban taba hawa titi fayau ba motoci irin yau ba, ni din ce kawai ban gadamar fitowa da wuri ba."
A karo na biyu ya sake dubanta da sauri ya danyi shiru na dan lokaci sannan ya kawo gwauron numfashi ya gyara zama yace " Ance min in jiraki za'a miki dan interview na yan mintuna kuma a daukeki aiki a baki ofis kai tsaye, koda bansanki ba amma nasan tabbas wanda ya tsaya miki babba ne don ban taba ganin inda akai hakan ba sai akanki don wasu da wuya suke neman aikin basu samu ba wata kila hakan ne yasa kike wani ji dakai kina gadara aikin ma ba wani damunki yayi ba."
Ta tsuke baki sanda ya kawo karshen zancen nashi tace " Gskyne ba damu na yayi ba kusan ma ince maka tilastani akai sbd ansan nice zan taimaka muku ba kune zaku taimaka min ba, batun wanda ya tsaya min kuwa koda a fadar shugaban kasa ya nema min aiki ba wanda ya isa ya hana bare nan."
Tayi nuni da ofis din a wulakance.
Ahmad ya sake binta da kallo a zuciyarsa yace " Wannan tafi ni bala'i."
Ya gyara zamansa tare da jawo laptop din dake gabansa ya mayar da hankalinsa gareta jim kadan ya dago kai yace " Meye sunanki?? "
Kanta na duban tebirin dake gabanta tace " HUMAIRA ".
ya danyi shiru kadan kamar me sauraron kara jin wani abu daga gareta, jin tayi shiru yasashi ture laptop din daga gabansa ya dubeta yace " Yakamata kiyi min adalci, kin bata min lokaci a zuwanki amsa tambayar ma sai kin sake bata min wani lokacin??"
Au wai kana nufin full name?? To sunana HUMAIRA ISMAIL.
Ta fada tana me kallonsa.
Ya jawo laptop sanda yayi tsaki kasa-kasa.
Meye level din karatunki??
Ta amsa da cewa " Masters degree ".
Yayi saurin dubanta cikin mamaki a ransa ya sake maimaitawa ( masters ) tab!!!!!
Wacce jami'a??
Ya sake tambayarta kansa nakan laptop din.
Ta dan kauda kanta kadan tace " oxford university- ENGLAND."
Bai san sanda ya sake dubanta ba cikin mamaki, A yarinya dole kiyi girman kai!! Ya fada a zuciyarsa.
Yayi saurin kauda kada ta fahimci halin da yake ciki yace " kinzo da takardunki ne??"
Babu bukatar zuwa dasu 2nda ba maular aiki nake ba dazan rinka yawo da takardun makarantaba hakanan...
Bala'i!!!! Lallai wannan tafi ni masifa.
Ya danyi shiru zuwa jimawa yace " last question!! Relationship??"
Tayi shiru kamar bata jiba ya sake maimaitawa da hausa da fadin " budurwa, bazawara ko matar aure?? wannan abu ne da dole a sani a duk inda mace zatai aiki a duniya.
Fuskar Humaira tayi saurin canjawa izuwa yanayi na damuwa tace " Don Allah kasa UNKNOWN kawai."
Ahmad ya hade rai cikin takaici ya shafa kansa " Wai ke wace irin mutum ce don Allah ?? Ya kike meman kisani ciwon kaine?? baki ma san ke budurwa ce ko bazawara ko matar aure ba?? "
Tayi saurin gyada kai tace " Eh bani da tabbacin zama daya daga cikinsu."
Ahmad ya mike cikin tsawa yace " wallahi karyane hakan baya taba yiwuwa dole a samu kina daya daga cikin wadannan azuzuwan ".
Ta mayar masa da martani da cewa " ba wani dalili da zaisa inyi maka karya 2nda ba aljanna zaka bani ba don haka karka kara karyatani akan abinda baka sani ba.
Ta dubeshi hawayen dake idonta suka yi gaggawar zubowa ta dora da cewa:
" Na rantse da Allah idan nace maka ni budurwace nayi karya!! Idan nace maka ni bazawara ce nayi karya!! Haka idan nace matar aure ce ni karya nake!! Ni kaina bansan da sunan da zan kira kaina ba.
Ahmad wanda fusata ta sashi mikewa yayi saurin komawa ya zauna idonsa ya zaro sbd mamaki, da AL'AJABI zuciyarsa ta fara sake-saken tayaya ma hakan zata faru?????????
Hmmm this my question 2 u my fellowers..
KO KUNSAN ANSAN..?.