Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta musanta
zargin da tsohon mai baiwa shugaban kasa
shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo
Dasuki yayi mata cewa ta hana shi fita waje
duba lafiyarsa duk da cewa Kotu ta bashi izini,
A wata sanarwa da Kakakin hukumar, Tony
OPUIYO ta fitar a jiya Alhamis ta bayyana
zancen na Mista Dasuki a matsayin cin fuska da kokarin bata mata suna,
Tace gaskiyar abinda ya faru shine Mista
Dasuki yaki amsa gayyata ne da wani kwamiti
da gwamnatin ta kafa domin binciken wasu
kudade Dala Bilyan Biyu da tsohuwar Gwamnati
ta kashe wajen sayo wasu makamai,
Ta kara da cewa kwamitin ya gayyaci Sambo
Dasuki domin ya bata bayanin abinda ya sani
dangane da wannan batu da ya faru a lokacin
sa amma sai yayi watsi da gayyatar,
A cewar hukumar ba wai ta takurawa Dasuki ba
ne kamar yadda yayi zargi, kawai dai ta lura
yana neman dojewa binciken da ake yi masa ne
wanda hukumar ba zata yarda ba,
“shi yasa muke bin hanyoyin da doka ta bamu
domin tilasta shi ya amsa gayyatar ” inji DSS
A nashi martanin game da wannan sanarwa na
DSS, tsohon mashawarcin shuganan kasar,
Kanar Sambo Dasuki yace babu wani kwamiti
da ya taba gayyatar sa akan sayen makamai da
tsohuwar Gwamnati tayi,
Mista Dasuki ya kara da kalubalanatar hukumar
da cewa “Wannan kwamiti a karkashin ofishin
mai bawa shugaban kasa shawara akan
harkokin tsaro yake ba ofishin DSS ba”
Title :
Abinda Yasa Muka Kewaye Gidan
Sambo Dasuki – DSS
Description : Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta musanta zargin da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki yayi m...
Rating :
5