Abdullahi bn Muhammad bn Ubaid ya ruwaito tare da isnadinsa zuwa ga Waheeb bn Al-wardi cewa:
"Watarana Qazamin nan Iblees ya bayyana awajen Annabi Yahya bn Zakariyya (alaihimas salam) yace masa: "Nazo ne don inyi maka Nasiha"
Sai Annabi Yahya (as) yace masa "QARYA KAKEYI, KAI BABU WATA NASIHAR DA ZAKA YI MIN. SAI DAI INA SO KA BANI LABARI GAME DA 'YAN ADAM NE".
Sai Qazami Iblees yace : "Ai su ('Yan Adam) awajenmu sun kasu guda uku ne.
Kashi na farko sune wadanda suka fi wahalar damu. Zamu zo ma 'dayansu, Har sai mun fitineshi mun samu cikakkiyar dama akansa, mun sanyashi ya aikata zunubi, Sannan sai kuma ya fara Istighfari yana tuba awajen Allah.
Har sai ya 'bata mana duk abinda muka samu daga gareshi. Sannan sai mu dawo gareshi, shi ma sai ya dawo (yaci gaba da Istighfari). Mu bamu fidda rai daga gareshi ba, Kuma bamu samu biyan bukatarmu awajensa ba. Don haka muna cikin wahala tare dashi".
Amma kashi na biyu, su yadda suke ahannunmu kamar yadda Qwallon Qafa take ahannun Qananan yaranku ne. Muna jujjuyasu duk yadda muka ga dama. Wadannan mun gama dasu".
Amma kashi na Qarshe, sune irinka Ma'asumai (Wadanda Allah ya riga ya kiyayesu) bamu iya samun dama akansa har abada".
Sai Annabi Yahya (as) yace masa "DUK DA HAKA, SHIN KA TA'BA SAMUN WATA DAMA AKAINA KUWA?".
Sai Qazamin yace : "A'a. Sai dai sau daya ne rak! Watarana an kawo maka abinci zaka ci. Ban gushe ba ina Qawatar maka da abincin nan har sai da kaci abincin nan da yawa. Fiye da yadda kake nufi. Sai barci ya daukeka awannan daren baka samu damar tashi cikin dare kayi Sallah kamar yadda ka saba yi ba".
Sai Annabi Yahya (as) yace: "NI KUWA HAR ABADA BA ZAN SAKE CIN ABINCI IN KOSHI BA".
Sai shi kuma Qazami Iblees yace : "Ni kuwa har abada ba zan sake yiwa wani 'Dan Adam nasiha ba".
ADUBA : AAKAMUL MARJAAN shafi na 212.
ZAUREN FIQHU :
******************
Tunda mu ba Ma'asumai bane. babu abinda yafi dacewa garemu illa mu dawwama cikin Istighfari da Zikiri da Salatin Annabi (saww) da yawan karatun Alqur'ani. Da haka ne zamu gagari Qazamin nan Iblees babban makiyinmu.
Allah yasa mu dace, Aameen.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.
Title :
Ziyarar Da Shaitan Ya Kaima Annabi Yahya Bn Zakariyya (AS)
Description : Abdullahi bn Muhammad bn Ubaid ya ruwaito tare da isnadinsa zuwa ga Waheeb bn Al-wardi cewa: "Watarana Qazamin nan Iblees ya bayyana a...
Rating :
5