Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun kaddamar da wani kwamiti na musamman, domin yi wa dokokin jihohin garambawul.
Kwamitin na manyan jami'an shari'a da sakatarorin gwamnati zai yi nazarin yadda za a sabunta dokoki ne domin fuskantar manyan laifuka a yankin.
An kaddamar da kwamitin ne a taron da manyan Alkalan jihohin arewacin kasar ke yi a Kaduna.
Kazalika, dukkan manyan Alkalan da suka halarci taron sun amince cewa dole a sabunta bangarorin shari'ar yankin na arewa mai fuskantar kalubalen tsaro a yanzu.
Title :
Za a yi wa dokokin jihohi garanbawul
Description : Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun kaddamar da wani kwamiti na musamman, domin yi wa dokokin jihohin garambawul. Kwamitin na manyan ja...
Rating :
5