Shugabannin Fulani a yankin kudu maso yammacin Najeriya sun shirya tsara yin rijistar Fulanin da ke kiwon dabobbinsu a yankin, domin magance rikici.
Sun kuma ce yin rijistar zai sa a san kowanne Bafillace da inda ya fito da kuma wajen da ayke gudanar da kiwonsa don samun bayani kansu a duk lokacin da ake zarginsu da abinda bai dace ba.
Wannan ya zo ne bayan samun rashin jituwa tsakanin Fulani makiyaya da Yarbawa manoma a sakamakon sace tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Cif Olu Falae, wanda sai bayan wasu kwanaki aka sako shi.
Lamarin dai ya janyo kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta soma yin kiran Fulani su fice daga yankinsu.
An sha samun rikice-rikice tsakanin Fulani da Makiyaya a jihohi daban-daban na Najeriya wanda haka ke zama barazana ga tsaron kasa a wasu lokutan.
Title :
Za a fara rijistar Fulani don magance rikici
Description : Shugabannin Fulani a yankin kudu maso yammacin Najeriya sun shirya tsara yin rijistar Fulanin da ke kiwon dabobbinsu a yankin, domin magance...
Rating :
5