Hukumar gudanar da gasar cin kofin firimiyar Nigeria, ta
tsayar da ranar Laraba domin cigaba da buga wasannin
mako na 34 na gasar.
A ranar Lahadi ya kamata a buga wasannin mako na 34,
amma sakamakon karawa da Nigeria ta yi da Burkina
Faso ya sa aka dage wasannin.
Nigeria ta ci Burkina Faso 2-0 a Fatakwal a ranar Asabar a
wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka ta 'yan
wasan da ke taka leda a gida.
Burkina Faso za ta karbi bakunci Nigeria a wasa na biyu a
ranar 25 ga watan Oktoba a Ouagadougou.
Haka kuma hukumar ta dage karawa tsakanin Sunshine
Stars da Rangers a ranar Larabar, sakamakon 'yan wasan
Sunshine Shida suna tare da tawagar kwallon kafar
Nigeria.
Gajerin wasanni mako na 34 da za a buga:
El-Kanemi v Giwa FC
Wikki v FC Ifeanyiubah
Heartland v Sharks
Shooting Stars v FC Taraba
Nasarawa Utd v Enyimba
Kwara Utd v Bayelsa Utd
Abia Warriors v Lobi Stars
Wolves v Akwa Utd
Sunshine Stars v Rangers
Dolphins v Kano Pillars
Title :
Za a cigaba da Firimiyar Nigeria ranar Laraba
Description : Hukumar gudanar da gasar cin kofin firimiyar Nigeria, ta tsayar da ranar Laraba domin cigaba da buga wasannin mako na 34 na gasar. A rana...
Rating :
5