A yau Talata ne ake sa ran majalisar dattawan Najeriya
za ta ci gaba da aikin tantance mutanen da Shugaba
Muhamadu Buhari ya tura ma ta, domin nada su
ministoci.
A makon jiya dai majalisar ta tantance, tare da amincewa
da nadin mutane 18 daga cikin mutane 36, da Shugaban
ya tura sunayensu ga 'yan majalisar.
Sai dai kuma majalisar ta karbi korafe-korafe kan wasu
daga cikin wadannan mutanen.
Daga cikin irin wadannan mutane da ake korafi akan su
sun hada da tsohon gwamnan Ribas Rotimi Amechi.
Sauran mutanen da ake da korafi akan su, sun kuma
hada da Aishatu Abubakar daga jihar Sokkoto da kuma
Hajiya Khadijah Abba Ibrahim daga jihar Yobe