Kungiyar gwamnonin juhohin Najeriya da
kamfanin NNPC da ke kula da hadahadr man
kasar, sun kulla wata yarjejeniyar dakile
hanyoyin da ake bi wajen satan man kasar.
Satar mai da fasa bututu
man da ke kwarara zuwa wasu sassa kasar, na
daga cikin matsalolin da ke wa arzikin Najeriya
zagon kasa wajen bunkasa.
Sai dai masu fashin baki a harkokin yau da kullum
sun ce, gwamnonin na Najeriya ba su da cikakken
hurumin dakile wannan matsala kamar yadda
jami’an tsaro ke da shi wajen kare dukiyar kasa.
“Wannan mataki zai taimaka, amma ba zai
dakatar da wannan aiki na assha ba domin satar
mai da ake yi ba kaiwa daga bututu ba ne ake yi
ba, akwai satar mai da ake a cikin rijiyoyinmu da
ke cikin teku.” A cewar Yusuf Tuga, wani masani a
fannin mai.
Sai dai a cewar Tuga, inda gwamnonin za su fi
taimakwa, shi ne ta hanyar samawa matasa aikin
yi da sa ido a kananan hukumomi ta inda bututun
mai ke ratsawa.
Baya ga satar mai a cikin gida, masanin ya ce
akwai bukatar a samu hadin kan kasashe
makwabta irinsu Ghana domin ana fakewa da su
wajen satan man Najeriya.