Yayinda 'yansandan Najeriya suka yi ikirarin
cafke wadanda suka yi garkuwa da Chief Olu
Falae su kuma 'yansandan fararen kaya da ake
kira DSS sun ce sun cafke wasu da suke zargi da
aikata laifin.
Mr. Solomon Arase babban
sifeton 'yansandan Najeriya yace rundunarsa ta
cafke mutane biyar cikin mutane takwas da ake
zargin su ne suka yi garkuwa da tsohon sakataren
gwamnatin tarayya Chief Olu Falae.
Kusan bayan awa 24 kacal da sanarwar
'yansandan ita ma hukumar 'yansandan farin kaya
ko DSS a takaice ta ce ta cafke wasu mutanen
daban bisa zargin su ne suka aikata yin garkuwa
da Chief Falae.
Yayinda 'yansanda ke cewa sun damke nasu ne a
jihohin Neja da Ekiti da Ondo ita kuma DSS ta ce ta
cafke nata ne a jihar Kogi.
Da Muryar Amurka ta tammbayi kakakin
'yansandan ko basa aiki kafada da kafada tare da
DSS sai tace zata yi magana ne kawai akan
wadanda 'yansanda suka cafke. Tace amma
babban sifetonsu ya tuntubi DSS da su basu
wadanda suka kama domin su hadasu su kai kotu.
Amma Dr. Muhammad Dengel wani kwararre
akan tsa'anin tsaro a Najeriya yana ganin babu
hadin kai tsakanin hukumomin biyu. Babu kuma
fahimmata tsakaninsu. Yace yakamata a zauna a
dubi sha'anin tsaro a kasar.
Title :
Yansanda da DSS Sun Yi Ikirarin
Cafke Wadanda Suka Yi Garkuwa da
Falae
Description : Yayinda 'yansandan Najeriya suka yi ikirarin cafke wadanda suka yi garkuwa da Chief Olu Falae su kuma 'yansandan fararen kaya da a...
Rating :
5