Duk wanda ya karanci tarihin wannan Annabi mai girma, Ma'abocin falala da fifiko mai girma, kuma ma'abocin kyawawan siffofi da halaye, zai tarar cewa Shi Shugaba (saww) bai taba aibunta kowa ba, kuma bai taba tauye ma wani mai girma girmansa ba.
Sai dai ko yaushe kalmominsa suna cike da shiriya da wa'azantarwa da bisharori ga Sahabbansa. Har sai da ya zamanto kalmominsa sun zama tamkar Sabulu ko magani mai wanke zukatan Sahabbansa har ma dukkan Talikai baki daya.
Kuma kalmominsa sukan Qara ma dukkan wanda ya sauraresu himma da Qwazo akan abinda yake yi na taimakon addininsa.
Wannan ita ce hanyarsa, kuma ita ce shiriyarsa acikin zamansa da mutanensa (saww).
Acikin wani hadisi Manzon Allah (saww) yace:
"DUK WANDA YAYI MUKU ABIN ALKHAIRI TO KU RAMA MASA. IDAN KUMA BAKU DA IKO TO KUCE MASA "ALLAH YA SAKA MAKA DA ALKHAIRI".
Acikin wani hadisin kuma yana yabon babban Masoyinsa, Surukinsa kuma Khalifansa na farko, Manzon Allah (saww) yace:
"WANDA YAFI KOWA AMINCE MIN ACIKIN DUKIYARSA DA ABOKANTAKARSA SHINE ABUBAKRIN. DA ACHE ZAN RIKI BADA'DI ACIKIN MA'ABOTA DORON QASAR NAN, DA ABUBAKAR NE ZAN RIKA AMATSAYIN BADA'DI NA".
(Imamu Muslim ne ya ruwaitoshi).
Akan Sayyiduna Umar kuma, Manzon Allah (saww) yace:
"ALLAH YA SANYA GASKIYA AZUCIYAR UMARU DA HARSHENSA".
Akan Sayyiduna Uthman kuma, yace: "ALLAH YANA JIN KUNYAR UTHMAN".
Akan Sayyiduna Aliyu kuma yace:
"YA ALLAH KASO DUK MAI SONSA, KUMA KAQI DUKKAN MAI QINSA"
Akwai wani Sahabi wanda ya shahara sosai wajen juriya da kwazo wajen gudu da Qafarsa zuwa wajen Jihadi ko kuma bin sawun barayi idan sukayi sata. Ana kiransa SALAMAH IBNUL AK-WA'I.
Shima Manzon Allah (saww) ya yabeshi yana cewa:
"MAFIFICIN MAHAYAN DAWAKANMU AYAU, SHINE ABU QATADAH. KUMA MAFIFICIN MAYAQANMU MASU TAFIYA A QASA SHINE SALAMAH".
(Muslim ne ya fitar da hadisin).
Acikin mutanen madinah Akwai gidan Kawunnan Manzon Allah (saww). Su ma ya yabesu yana cewa:
"MAFIFICIN GIDAJEN MUTANEN MADINA, SHINE GIDAN BANUN NAJJAR".
(Muslim ne ya fitar da hadisin).
Saboda kasancewar mutanen Madeena sunyi rigaye wajen karbar Musulunci da taimakonsa da kuma bayar da mafaka ga sauran Musulman farko, Manzon Allah (saww) yana mutukar Kaunarsu.
Ga abinda yake cewa akansu :
"NA RANTSE DA WANDA RAINA YAKE KARKASHIN IKONSA, DA ACHE SAURAN MUTANE ZASU SHIGA WANI GEFE, KUMA MUTANEN MADINA MA SU SHIGA WANI GEFE, WALLAHI DA ZAN SHIGA GEFEN MUTANEN MADINA NE.
"DA BA DON HIJIRAH BA, DA ZAN KASANCE DAGA CIKIN MUTANEN MADINA NE".
"YA ALLAH KAJI QAN MUTANEN MADINA, DA 'YA'YAN MUTANEN MADINA, DA 'YA'YAN-'YA'YAN MUTANEN MADINA".
(Imamu Ahmad ne ya ruwaito hadisin acikin Musnad".
Haka ake son kowanne shugaba ya zama yana yaba ma Mutanensa wadanda suka aikata abin kirki. Domin yin hakan zai Qara musu kwazo da himma, kuma zai Qara ma Shugaban nasu mutunci awajensu.