DASHISHI
========
• Alkama
• Kifi
• Nama
• Mai
• Maggi Gishiri
• Attaruhu
• Albasa
• koran tattasai
• curry
• kabeji,karas
• koran wake
ki kai alkamarki a surfa miki ki wanke ki shanya ta bushe,a barzo miki a inji,ki tankade garin ciki ko ya yake,ki yayyafa ruwa a ciki ki turara kamar dambu sai ki sauke bayan minti 30,ki gyara busasshen kifin ki zuba a ciki idan kuma nama ne sai kin sulalashi da albasa da magi sai ki dakashi ki zuba a kai,in kuma duka kk so sai ki hada,ki yanka koran tattasai da karas koran wake kabeji albasa,ki jajjaga attaruhu ki zuba,kisa magi curry gishiri da mai ki jujjuya ki kuma dorawa a kan wuta ki turarashi,idan ya turara ki sauke,shikenan sai ci