TAMBAYA TA 1734
********************
Assalamu alaikum, Allah shi saka ma Malam da alkhairi. Don Allah Malam shin ya halatta Mace ta wanki gawar Mijinta bayan ya rasu, Alhali ita tana da haila ko Janabah?
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Eh ya halatta. Domin kuwa shi Mumini ba ya zama Najasa saboda haila ko Janabah. Ga hadisi nan wanda Imamul Bukhariy da Muslim da Ahmad da Tirmiziy duk sun ruwaito Manzon Allah (saww) yace:
"MUMINI BA YA ZAMA NAJASA".
Amma wasu daga cikin Malamai sun karhanta ma Mai Janabah yin wankan Gawa.
Idan Mutum Mumini ya rasu, Matarsa Musulma Mumina tana daga cikin wadanda sukafi dacewa su wanke gawarsa. Mutukar dai ta san yadda ake yin wankan.
WALLAHU A'ALAM.