A Jamhuriyar Nijer daliban makarantun boko sun
gudanar da zanga-zanga a yau litinin a titunan
Yamai domin nuna bacin rai a game da abinda
suka kira rashin cika alkawali akan maganar wasu
bukatun da suka gabatar hukumomin ilimi.
Zanga zangar ta samo asali
ne daga kungiyar daliban makarantun kimiya da
sana’ar hannu UIEPTN bayan da ta kira magoya
bayan ta domin nuna bacin rai akan matsalolin da
suka hada da matakin korar wasu dalibai da
hukumomin ilimi suka dauka da karancin dakunan
karatu da karancin malamai.
Sauran matsaloloin na su sun hada har da
karancin samun karatu da rashin ban daki da dai
sauransu,
Mataimakin Sakataren kungiyar dalibai ta UIEPTN
Idi Mousa Uamrou ya ce shirin da suka ji daga
gwamnati bayan wa’adin mako guda da suka
bayar ne ya sa suka bazama akan tituna.
‘‘Cikin watan da ya wuce, tun kwanan wata na
bakwai, muka fiddo matsalolnmu muka ce musu
ga abinda muke so, amma mun ba da shawara a
kira mu a yi shawara da mu, sai aka wayi gari
wannan satin ya wuce babu wata shawara da aka
yi’’ In ji Umarou .
Jami’in hulda da ‘yan jarida a makaranta Jibril Na
Malka, ya ce ba za su ce uffan kan wannan
matsala ba domin a cewar shi ana tattaunawa da
daliban.
Wannan zanga zanga dai ta janyo arangama da
tsakanin daliban da jami ;an tsaro wadanda suka
yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa
dalibai.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, zanga
zangar ta bazu zuwa illahirin makarantun
sakandaren birnin Yamai inda dalibai suka yi ta
fashe fashe da kone konen tayoyi har da wasu
motoci guda biyu.
Gwamnan Jahar Yamai Hamidu Garba, ya yi Allah
wadai da wannan lamari kamar yadda za ku ji
bayan kun kammala sauraron wannan rahoto da
wakilin Muryar Amurka a Yamaia Souley
Moumouni Bramah ya aiko mana: