Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin
Duniya ta ce yawan 'yan gudun hijira da suka shiga Turai
cikin wannan shekarar ya kai 600,000 ya zuwa yanzu.
Wannan adadi dai ya ninka yawan 'yan gudun hijirar da
suka shiga Turai bara har sau uku.
Alkalumma sun nuna cewa yawancinsu sun shiga Girka
daga Turkiyya ta teku.
Wakiliyar BBC ta ce alkalumman hukumar 'yan gudun
hijirar na cewa fiye da rabin 'yan gudun hijirar sun fito ne
daga kasashen da ke fama da tashin hankali kamar su
Syria da Afghanistan da kuma Iraki.
Wani kason na 'yan gudun hijirar sun tsallaka Turai ne ta
tekun Bahr Rum daga Libya zuwa Italiya.