Wasu dauke da muggan makamai da ake zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun aukawa garin Gaidam da ke jihar Yobe.
An yi ta barin wuta a garin, lamarin da ya sa mutane suka fake a gidajensu.
Wani mazaunin Gaidam ya shaida wa BBC cewa "Karfe biyar da rabi na yamma 'yan Boko Haram suka shigo mana. Sai aka soma harbe-harbe tsakaninsu da sojoji. A lokacin mun shige gida mun boye."
"A yanzu maganar da nake yi, babu sojoji sai 'yan Boko Haram a cikin garin. Muna jin kabbararsu suna yawo da motoci a cikin garin," in ji mazaunin Gaidam.
A duk ranar Talata ake cin kasuwa a garin na Gaidam.
'Yan Boko Haram sun sha kai munanan hare-hare a garin na Gaidam da ke kusa da iyaka da jamhuriyar Nijar.
A safiyar ranar Talata ma, 'yan Boko Haram sun hallaka mutane 17 a Damaturu babban birnin jihar ta Yobe.