FUNKASO
• fulawa
• alkama
• ruwa
• kanwa
• yis
• mai
• wake
ki tankade garin alkama ko fulawarki,ko kuma ki hada duka idan na rabi rabi zakiyi sai ki sa garin alkama gwangwani biyu fulawa gwangwani biyu idan kina son wake sai kisa rabin gwangwani a niko miki tare xe kara laushin sa,sai ki kwaba da yis kamar kwabin fanke ki aje shi zai kumburo inya tashi sai ki buga shi sosai sai ki dansa kanwa,sai ki dora mai a wuta ki dinga gutsirar kullun kina fadadawa a bayan faranti ki huda tsakiyarsa ki sa a mai ki soya idan yayi ja ki tsame,zaki iya hadawa da farfesu.
Asma'u Garba