Ya kamata ace an hukunta Hector Moreno a ketar da ya
yi wa dan kwallon Manchester United, Luke Shaw in ji
tsohon alkalin wasa Pierluigi Collina.
Alkalin wasa Nicola Rizzoli bai dauki mataki kan ketar da
dan wasan PSV Eindhoven, Moreno ya yi wa Shaw a
gasar cin kofin zakarun Turai da suka yi a watan jiya ba.
Collina ya ce mun sha tunatar da alkalan wasa da su kula
da kuma maida hankali kan hukunta 'yan wasa masu irin
wannan dabi'ar.
Ya kuma ce babu wanda ya tsinkayi abinda ya faru har da
su kansu 'yan wasan da suke buga karawar a lokacin.
Collina dan kasar Italiya wanda ya yi ritaya daga
alkalancin wasa a shekarar 2005, ya ce abinda yake daure
wa mutane kai kenan a inda aka ci gaba da taka leda ba
tare da an tsaida wasan ba nan take.
Title :
Ya ci ace an dauki mataki kan raunata Shaw - Collina
Description : Ya kamata ace an hukunta Hector Moreno a ketar da ya yi wa dan kwallon Manchester United, Luke Shaw in ji tsohon alkalin wasa Pierluigi Co...
Rating :
5