Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya bukaci 'yan wasansa
da su kara kaimi domin doke Bayern Munich a gasar cin
kofin zakarun Turai da za su yi ranar Talata.
Wenger ya ce idan har suka samu nasara a kan Bayern
hakan zai karfafa musu gwiwa da kuma tabbatar da
cewar ba a fitar da su daga gasar da wuri ba.
Arsenal wacce take mataki na biyu a kan teburin Premier,
ta yi rashin nasara a wasanni biyu da ta buga da Dinamo
Zagreb da kuma Olympiakos a gasar ta zakarun Turai.
A tarihi Gunners ta yi rashin nasara a hannun Bayern a
wasanni biyu a gida, yayin da ta je Jamus ta ci wasa
daya ta kuma yi kunnen doki da su a karawa daya.
Za a yi wasan ne na ranar Talata a gidan Arsenal wato
Emirates.