Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da
hafsoshin sojan Najeriya sunyi wata ganawa ta
musammam, tare da shugabannin soji na Amurka
wanda suka ziyarci kasar, inda aka bayyana cewa
dakarun Amurka sama da 300 ne suka isa kasar
Kamaru, ‘dauke da kayan aiki domin taimakawa
Najeriyar da makwabtanta wajen yaki da Boko
Haram.
Tawagar wadda ke dauke da
kwamandan soji mai kula da kasashen Afirka
janar David Rodriguez da kuma mataimakiyar
sakatariyar tsaro ta kasar Amurka Amanda Doris,
sun sami bayani daga shugaba Buhari wanda ya
basu tabbacin cewar a watan Disamba ne ake sa
ran za’a kammala yaki da ‘yan kungiyar Boko
Haram, kuma a karya lagon su yadda ba zasuyi
wani tasiri na tayar da zaune tsaye a Najeriya ba.
Akan haka ne wakilin Muryar Amurka Umar
Farouk Musa, ya tuntubi wani soji kuma mai
sharshi kan al’amurran tsaro a Najeriya, Janaral
Abdurrazak Umar mai ritaya, domin jin tsokacinsa
dangane da kokarin kammala yaki da Boko Haram
a watan Disamba.
Sai dai Abdurrazak dai yace yaki ko karawa da
‘yan ta’adda ko ‘yan yakin sunkuru ba dai dai yake
da yakin fito na fito ba, yaki da ‘yan ta’adda abu
ne mai wahala domin su zasu mamayi mutane ne
su shigo suyi barna, idan aka nemi a kara dasu sai
su gudu. Ya kara da cewa yana da hatsari a fitar
da lokaci guda ace za’a durkushe su, ba lalle bane
a cimma buri ba.
Daga karshe janaral ya bayar da shawarar abinda
yakamata ayi don samun galaba kan ‘yan bindigar
masu tayar da kayar bayan, inda yace abu biyu
za’ayi na farko shine a karfafa rudunonin sojoji da
jami’an tsaro a fadin kasar, na biyu shine abu
mafi muhimmamci wanda yake samun lagon su ko
samun sirrunsu, ta hada bayanan sirri, kamar
inda suke me suke shiryawa da makamantansu.
Title :
Watan Disamba Ake Sa Ran Kawo
Karshen Boko Haram
Description : Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da hafsoshin sojan Najeriya sunyi wata ganawa ta musammam, tare da shugabannin soji na Amurka wa...
Rating :
5