Tawagar Golden Eaglets ta Nigeria ta kai zagaye na gaba
a gasar cin kofin duniya bayan da ta lallasa mai
masaukin baki Chile da ci biyar da daya.
Samuel Chukwueze da Victor Osimhen sun ci kwallaye
biyu kowannensu a yayin da Kelechi Nwakali shi ma ya
zura kwallo daya.
Marcelo Allende ne ya farke wa Chile kwallo daya.
Nigeria ta tsallake zuwa zagaye na gaba tare da Koriya ta
Kudu a yayin da Chile za ta hadu da Amurka a ranar
Juma'a domin daya daga cikinsu ta tsallake zuwa mataki
na gaba.
Title :
U17: Nigeria ta lallasa Chile
Description : Tawagar Golden Eaglets ta Nigeria ta kai zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya bayan da ta lallasa mai masaukin baki Chile da ci biyar d...
Rating :
5