Tawagar matasa 'yan kasa da shekaru 17 ta Nigeria ta
fara kare kambunta da kafar dama, bayan da ta doke ta
Amurka da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a ranar Asabar a
Chile.
Tawagar karkashin jagorancin kociya Emmanuel
Amuneke, ta ci kwallayenta biyu ne bayan da aka dawo
daga hutun rabin lokaci ta hannun Chukwudi Agor da
kuma Victor Osimhen.
Da wannan nasarar Nigeria tana mataki na daya a rukunin
farko da maki uku, bayan da Chile da Croatia suka tashi
kunnen doki 1-1.
Sauran wasannin da aka kara a ranar Asabar din Guinea
da Ingila suma 1-1 suka yi, sai Korea ta Kudu da ta ci
Brazil daya mai ban haushi.
Kasashe hudu ne ke wakiltar Afirka a gasar da suka hada
da Mali da Nigeria da Guinea da kuma Afirka ta Kudu.
Ga wasannin da za a buga a ranar Lahadi:
Belgium vs Mali
Australia vs Germany
Honduras vs Ecuador
Argentina vs Mexico